Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bayar da hujjar cewa akwai bukatar a kawo karshen tallafin man fetur a kasar nan, yana mai cewa idan har ba a yi gaggawar cire tallafi ba, to zai hakala ‘yan Nijeriya.
A cewarsa, sabuwar gwamnati ta yi hasashen cewa za a fuskanci adawa mai tsanani kan matakin da ta dauka na cire tallafin man fetur, amma ya lura cewa akwai bukatar dagewa wajen cimma wannan buri.
Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Talata lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar farko da ya hau kan karagar mulki a fadar gwamnati da ke Abuja, sai dai ya yi gargadin cewa Nijeriya na bukatar kawar da tallafin mai, idan ba haka ba tallafin zai kawar da al’ummar Nijeriya.
Ya jaddada cewa tsarin tallafin ba ya amfanar da talakan Nijeriya, sai dai yana tallafa wa rayuwar masu hannu da shuni. Ya tabbatar da cewa duk da adawar da ake sa ran masu cin gajiyar tsarin tallafin za su yi, Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu kasancewarsa mai kishin kasa zai magance barazanar da ake fuskanta a bangaren mai gaba daya.
“Tuni shugaban kasa ya yi sanarwa kan batun tallafin man fetur. Maganar gaskiya ita ce ko dai mu cire tallafi yanzu ko kuma tallafin man fetur ya kawar da al’ummar Nijeriya.
“A shekarar 2022, mun kashe dala biliyan 10 wajen tallafa wa rayuwar masu hannu da shuni, saboda ni da ku ba ma amfana da kashi 90 daga tallafin man fetur. Talakawa kashi 40 cikin 100 na ’yan Nijeriya kadan ne ke amfana kuma hakan babbar illar ce.
“Za mu fuskanci adawa mai zafi daga wadanda ke cin gajiyar badakkalar tallafin man fetur, amma hakan shi ya fi dacewa. Ku tabbata cewa shugabanmu mutum ne mai kwarjini da kuma yakini..
“A cikar lokaci za ku yaba da kyawawan manufofinsa ga al’umma. Batun tallafin man fetur za a tunkari matsalar gaba daya. Da zarar mun yi haka, zai fi kyau,” in ji shi.
Da yake tsokaci kan batun canjin kudaden kasashen waje, mataimakin shugaban kasar ya ba da tabbacin cewa “za mu durkusar da kudaden waje gaba daya.
Ya kuma bayyana cewa nan ba da dadewa ba Shugaba Tinubu zai fito da ajandar sabuwar gwamnatin da za ta amfani daukacin ‘yan Nijeriya.