Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II, ya ce, tsohuwar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ce ta yi sanadin tabarbarewar tattalin arziki da ‘yan Nijeriya ke fama da shi a yazun, ba wai gwamnatin da ta gaje shi ba ce, ta Shugaba Bola Tinubu.
Sarkin ya ce, gwamnatin Buhari a cikin shekaru takwas da ta yi, ta rugurguza tattalin arzikin kasar nan ba tare da sauraron shawarwarin masana ba.
Sanusi II, wanda tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN) ne, ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo ne a lokacin da yake jawabi ga dalibansa a taron karantarwa ta addinin Musulunci da ya saba yi.
Ya ce, ‘yan alfarma da suka mamaye gwamnatin Buhari, su suka janyo halin da ake ciki, inda ya buga misali da cewa, “Dan karamin yaron da ba shi da kwarewa” zai iya mallakar jirgin sama mai zaman kansa a karkashin gwamnatin da ta shude sabida yana samun Dala a kan farashin gwamnati sannan ya saida wa ‘yan kasuwar canji don samun ninkin riba.
Sanusi II ya kuma ce, karbo rancen da gwamnatin Buhari ta yi, ya gurgunta tattalin arzikin Nijeriya, mawuyaciyar rayuwar da ‘yan Nijeriya ke fuskanta a halin yanzu, da karyewar darajar Naira.
Don haka, ya bukaci ‘yan Nijeriya su yi hakuri da gwamnatin shugaba Bola Tinubu, wanda ya amsa jagorancin kasa a watanni uku da suka gabata.
Source: LEADERSHIPHAUSA