A karon farko a tarihin kafuwar Najeriya, an samu jihar da ta fara cin arzikin man fetur daga Arewa.(RMAFC )
Gwamnan jihar Kogi ya tabbatar da cewa sun karbi 13% da ake warewa jihohin da ke hako danyen mai RMAFC ta fara lissafi da jihar tsakiyar Arewacin Najeriyar ne bayan hako danyen rijiyar man Ibaji.
Maganar da ake yi, jihar Kogi ta samu kasonta na farko a matsayin jiha mai arzikin man fetur a Najeriya, a karon farko a Arewacin kasar nan.
Jaridar The Nation ta rahoto Gwamna Yahaya Bello yana bayanin cewa gwamnatin jiharsa ta karbi kaso daga cikin 13% da ake warewa jihohi masu mai.
Mai girma Yahaya Bello ya yi wannan bayani a wajen taron majalisar zartarwa na jiha wanda aka saba yi duk mako a gidan gwamnati na Lugard House.
Gwamna Bello yace gwamnatinsa tayi abubuwan a-zo-a-gani, inda yace samun arzikin mai zai taimaka wajen cigaba da kawowa mutanensa cigaba.
A jawabinsa, Daily Trust tace Gwamnan ya nuna farin-ciki da wannan nasara da jihar ta samu.
A cewar Bello, gwamnatinsa ta samu lambar yabo da kyauttuka iri-iri saboda yadda suke tafiyar da mulki keke-da-keke kuma cikin gaskiya da amana.
“Mun sha wahala wajen kafa tarihin nan.”
Ba don gudumuwar mutanenmu da suka tsaya mana ba, da ba za mu iya kai wa ga nasarar nan ba.
Muna mika godiyarmu da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da jagorancin da ya yi, da kuma RMAFC da ta sa wannan ya tabbata.” – Yahaya Bello
Al’umma za su amfana da dukiyar Gwamnan ya yi alkawarin amfani da dukiyar da aka samu wajen gina makarantu, asibitoci, da tituna, sannan a tallafawa marasa karfi tare da inganta tsaro.
Kwamishinan yada labarai na jihat Kogi, Kingsley Fanwo yace kudin sun fara zuwa ne a lokacin da Gwamna yake yin ayyukan da za a tuna da shi nan gaba.
Ya aka yi Kogi ta samu fetur?
Hukumar RMAFC mai kasafin dukiyar kasa da albashi ta sa Kogi a matsayin jihar da take da arzikin mai, don haka za ta rika amfana da kashi 13% duk wata.
Dama can an yi alkawari jihar za ta fara karbar kasonta a wannan kudi idan rijiyar man Ibaji ya fara aiki, kuma yana kawowa asusun tarayya kudin-shiga.
Gwamnan Kwara ya nada Hadimai An samu rahoto a ranar Alhamis cewa mata 16 suka samu kujerun Masu taimakawa Mai girma Gwamna jihar Kwara wajen ganin cin ma manufofin SDGs.
A yanzu mata suke rike da 56.25% na kujerun Kwamishinoni da kuma 50% na mukaman Sakatarorin din-din-din a mulkin Abdulrazaq Abdulrahman.
Source:legithausang