Rahoton daga majalisar dinkin duniya yana tabbatar da cewa kwamitin sulhu na MDD ya bukaci sassan kasar Afghanistan da su dakatar da ricikin a tsakaninsu, da kuma kafa wata sabuwar gwamnatin da za ta iya kunshi kowa da kowa, da kuma kare hakkin mata.
A Sanarwar da ya fitar bayan taron da ya gudanar kan kasar ta Afghanistan, kwamitin ya nuna cewa, ya kamata a kare tsaron al’ummomin kasar da na sauran kasashen duniya.
A sa’i daya kuma, kwamitin ya jaddada muhimmancin yaki da ‘yan ta’adda a kasar, domin magance hare-haren da za a iya kai ga sauran kasashen duniya.
A jawabin farko da ya gabatar tun bayan da kungiyar Taliban ta kwace iko, shugaba Joe Biden na Amurka, ya gargadi kungiyar Taliban da cewa duk wani hari a yayin da ake saka da kwashe mutane, Amurka za ta mayar da martani mai karfi kuma cikin gaggawa.
Rahoton da muka samu ya tabbatar da cewa biden, wanda ke shan suka game da matakin janye dakarun na Amurka a Afghanistan, ya ce baya nadamar matakin da ya dauka, hasali ma ba zai sauya matsayinsa ba.
A wani labarin na daban rahoton dake shigo mana ya tabbatar da cewa, shugaban ƙasar afganistan Ashraf Ghani ya fice daga ƙasar inda wasu rahotannin suka ce ya tafi ƙasar Tajikistan, hakan kuwa yana zuwa ne a daidai lokacin da mayaƙan ƙungiyar Taliban suka yi wa birnin Kabul, babban birnin Afghanistan ɗin ƙawanya.
Har ya zuwa yanzu dai babu wani cikakken bayani dangane da abin da ya sanya shugaba Ghanin ya bar ƙasar, to sai dai rahotanni suna nuni da cewa ɗaya daga cikin buƙatun ƙungiyar ta Taliban shi ne shugaban ya bar mulki, don kuwa suna ganinsa a matsayin wanda ya ke ƙafar ungulu ga shirin tattaunawar sulhu da ake yi a ƙasar.
A ɓangare guda kuma kakakin ƙungiyar ta Taliban Suhail Shaheen ya ce suna fatan ganin an miƙa mulki cikin ruwan sanyi cikin ‘yan kwanaki masu zuwa, yana mai cewa ƙungiyar za ta kare haƙƙoƙin al’ummar Afghanistan ɗin ciki kuwa har da haƙƙoƙin mata, yana mai cewa ƙungiyar a shirye take ta bar duk wani wanda ya ke son barin birnin na Kabul da suka yi masa ƙawanya.
Wasu rahotannin dai suna nuni da cewa ɓangarori daban-daban na ‘yan siyasa da manyan jami’an gwamnatin ƙasar ta Afghanistan suna ci gaba da tattaunawa kan yadda za a magance rikicin da ya kunno kai a ƙasar, inda aka ce a gobe za a ci gaba da tattauanwar da ake yi tsakanin gwamnatin Afghanistan ɗin da tawagar ‘yan Taliban ɗin a birnin Doha na ƙasar Кatar.
A yau da rana tsaka ne dai ma’aikatar harkokin cikin gida a kasar Afghanistan ta sanar da cewa, mayakan Taliban sun fara shiga birnin Kabul ne a yau ta dukkanin bangarorin birnin.
Sannan kuma bayanin ya ce, bayan shiga birnin sun mamaye jami’ar Kabul da ke yammacin birnin, inda suka kafa tutocinsu a kan gine-ginen jami’ar, sannan kuma yanzu haka suna ci gaba da kara nausawa zuwa wasu sassan birnin.
Da jijjifin safiyar yau ne dai aka fara kwashe kayayyaki daga ma’aikatun gwamnati, kamar yadda kuma jami’ai da dama suka fice daga birnin.