Tsohon shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata mai wakiltar Yabe ta Arewa, Dr. Ahmad Lawan, ya tallafa wa al’ummar mazabarsa da kayan abinci kimanin buhuna 9000 na hatsi da shinkafa don rage radadin tsadar rayuwa a yankin.
Wannan matakin tallafin na Sanata Lawan, dadi ne a kan makamancinsa wanda Gwamnatin Tarayya da ta jihar Yobe ke yi wajen rage wa al’umma wahalhalun da suke fuskanta, sakamakon cire tallafin man fetur.
Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya kaddamar da tallafin kayan abincin, wanda Gidauniyar ‘SAIL’ ta dauki nauyin aiwatar da shi a cikin gundumomi 60 da ke Yobe ta Arewa.
Taron rabon kayan tallafin abincin ya gudana ne ranar Asabar, a Filin Kwallon Kafa da ke unguwar Katuzu a garin Gashuwa ta karamar hukumar Bade a jihar Yobe; wanda ya kunshi buhunan shinkafa 6000 da na gero 3000.
An raba tallafin ga kungiyoyin addinin musulunci, na Kirista, nakasassu da masu karamin karfi daga kananan hukumomi shida na Yobe ta Arewa. Bade, Nguru, Jakusko, Karasuwa, Yusufari da Machina.
A daidai lokacin da ake gudanar da Tattakin Arba’in Hussaini a kan hanyar Hussein (AS), tana yunkurin shirye-shiryen tarbar maziyartan.
A wani labarin na daban kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA – ya habarta cewa, Motocin da ke dauke da kayan masarufi na Tantin majalissar Ahlul-baiti (a.s) sun shiga kasar Iraki da birnin Najaf Ashraf kuma a daidai lokacin da kayayyakin hidimtawa masu tattakin aka aje shi a Tanti mai namba 206 ake rarraba kayayyakin da aken yi amfani da su a wannan wuri.
Wannan tawagar jerin gwanon na kasa da kasa ana shirya shi ne da kokarin Majalisar Ahlul Baiti (a.s.) da kuma taimakon masu yi wa Maziyarta Abi Abdullah Hussein (a.s) hidima ta hanyar da ta dace.