Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, NEMA, ta ce rumbun ajiyar abinci da aka wawashe a Abuja a ranar Lahadi ba mallakinta ba ne.
Da Safiyar ranar Lahadi, giajen jaridu da dama sun rahoto cewa, wasu matasa da ake zargin bata gari ne sun afka wani rumbun ajije abinci da ake kyautata zaton mallakar hukumar NEMA ne da ke unguwar Gwagwa a babban birnin tarayya Abuja domin kwashe kayan abinci saboda tsadar rayuwa da tabarbarewar tattalin arzikin da al’ummar kasar ke ciki.
Wasu mazauna unguwar sun bayyana cewa, matasan sun afka cikin rumbun ajiyar ne da misalin karfe 7 na safe, inda suka yi awon gaba da buhunan masara da sauran kayayyakin abinci.
Sai dai, a cikin wata sanarwa da jami’in hulda jama’a na NEMA, Ezekiel Manzo ya fitar, ya karyata rahoton cewa, rumbun mallakin hukumar ne.
A wani labarin na daban Jihar Gombe ta shirya karɓar baƙuncin Mataimakin Shugaban Nijeriya, Sanata Kashim Shettima, a ranar Litinin inda zai ƙaddamar da shirin samar da guraben ayyuka da janyo masu zuba jari daga waje (OTNI) tare da ƙaddamar da Cibiyar Horaswa da zaƙulo Hazikan Matasa (BPO).
Cibiyar ta BPO wacce ita ce ta farko a shiyyar Arewa Maso Gabas kuma irinta mafi girma a Nijeriya, an tsara zata samar da aƙalla guraben ayyukan yi 2,000 ga matasa masu basira da hazaƙa a Jihar Gombe bisa irin jagorancin hangen nesa na Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya.
Yanzu da aka kafa cibiyar ta BPO a Gombe, a Cibiyar Horar da Sana’o’i ta Amina Mohammed Skills Acquisition Centre da ke Bypass daura da hanyar Gombe zuwa Biu, jihar ta shirya zama cibiyar samar da kayayyaki, ta hanyar amfani da basira da hazakar matasanta.
Cibiya irin ta OTNI, hanya ce dake kawo sauyi a harkar kasuwanci da samar da fasahar ƙere-ƙere, kuma hanya ce mafi sauri da za ta samar da ayyukan yi ga matasan Jihar Gombe dama Nijeriya baki ɗaya.
A cewar sanarwar da Ismaila Uba Misilli, Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe ya fitar, ta hanyar shiga wannan shiri, gwamnatin Gwamna Inuwa Yahaya ta ƙara nuna aniyarta na samar da ayyukan yi masu ɗorewa da baiwa matasa damar bada gudumawa mai ma’ana ga ci gaban jihar.
Misilli ya ce, “Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya yana miƙa godiya ga Mai Girma Mataimakin Shugaban Ƙasan Kashim Shettima bisa goyon baya da jajircewansa wajen bunƙasa tattalin arzikin Jihar Gombe dama Nijeriya baki ɗaya, a daidai lokacin da yake shirin karɓar baƙuncin mataimakin shugaban ƙasan da sauran baƙi.”
Duba nan: Dalilin Da Yasa Kotu Ta Bada Umarnin Kamo Ado Gwamja
“Taron ƙaddamarwar zai gudana ne a ɗakin taro na ƙasa da ƙasa dake kan hanyar Gombe zuwa Bauchi da misalin ƙarfe 9:00 na safe, wanda zai samu halartar manyan masu ruwa da tsaki na gwamnati da masu zaman kansu daga ciki da wajen kasar nan.”