Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin N-Power har illa-masha-Allah.
Matakin na zuwa ne bisa wasu abubuwan da aka gano game da shirin wanda ba daidai ba.
A cewar gwamnati, daukan matakin dakatarwar na zuwa ne bisa gano wasu kura-kurai da suke makale a shirin, kuma, tunin aka kaddamar da bincike kan yadda aka sarrafa kudaden da aka fitar tun lokacin fara aiwatar da shirin.
Ministar kula da harkokin jin-kai da yaki da fatara, Betta Edu, ita ce ta sanar da hakan yayin da take magana ta cikin wani shirin labaran talabijin din ‘TVC’ a ranar Asabar, ta yi ikirarin cewa wasu da suke cin gajiyar shirin ba su zuwa wuraren da aka turasu aiki, amma har yanzu su na tsamamanin a biyasu alawus-alawus na wata-wata.
Edu ta kara da cewa wasu da suke cikin shirin sun kammala cin moriya tun 2022 amma har yanzu suna cikin jerin wadanda ake biya.
“Dole ne mu waiwaya baya mu duba shirin N-Power kuma mun gano akwai kura-kurai don haka mun dakatar da shirin a yanzu har zuwa lokacin da za a kammala gudanar da cikakken bincike kan yadda aka sarrafa kudaden shirin N-Power.”
Ta ce, dole su gano mutum nawa ne suke cikin shirin a halin yanzu da kuma bashin da ke tattare da shi tare da gano mutum nawa ne bashin ya shafa, a cewarta gabaki daya suna son sauya fasalin tarin N-Power da ma fadada shi.
“Abubuwa da dama su na kan faruwa. Mun samu mutanen da ya dace su fita daga cikin shirin tun shekarar da ta gabata amma har yanzu suna kan ikirarin cewa suna koyarwa.
“Wasu lokutan idan muka tuntubi makarantu ko wuraren da aka turasu aiki sai a tarar ba su zuwa ba su nan gaba daya.
Ba su aikin amma su na ta ikirarin cewa suna bin bashin alawus na wata tawas ko wata tara.
Kusan kaso 80 cikin 100 ba su aikin amma suna ta neman a biyasu albashi,” ta shaida.
Source LEADERSHIPHAUSA