Akalla kajin da yawansu ya kai rabin miliyan ne suka mutu sakamakon barkewar cutar murar tsuntsaye ta H1N1 a Burkina Faso.
Ministan albarkatun dabbobi a Burkina Faso Moussa Kabore ya shaidawa taron manema labarai a jiya Asabar cewa an gano bullar cutar ta murar tsuntsaye ce a karshen shekarar da ta gabata a gonaki 42 a wasu yankuna bakwai da ke tsakiya da kuma yammacin kasar.
Ministan ya kara da cewar, ya zuwa ranar 7 ga watan Janairu, baya ga kusan kajin dubu 500,000 da suka mutu sakamakon murar ta H1N1, an kuma lalata kwalayen kwai miliyan 1 da dubu 300.
A wani labarin na daban Babban mai shigar da kara na Haiti ya mika bukatar fara tuhumar Firaministan kasar Ariel Henry dangane da kisan gillar da aka yiwa tsohon shugaban kasar Jovenel Moise.
Hujjoji na ci gaba da karfafa wadanda ke zargin hannun Firaministan a kisan shugaba Jovenel Moise yayin wani farmaki da mahara suka kai gidansa watanni kusan 3 da suka gabata.
Cikin wata wasika wadda ke matsayin ta 2 da sashen shigar da karar ya gabatarwa gwamnati ya nemi hukumar shige da fice ta kasar ta haramtawa Firaminista Ariel Henry barin kasar a kowanne yanayi.
Wata shaidar baya-bayan nan ta nuna yadda Henry ya yi waya da babban wanda ake zargi da kisan shugaban na Haiti, lokaci kankani bayan farmakin da ya hallaka shugaban.
Wasikar mai dauke da sa hannun babban mai shigar da kara ta kasar ta kuma nemi izinin gurfanar da Firaministan don amsa tuhuma dangane da alakarsa da maharan na ranar 6 ga watan Yuli.
Tun a juma’ar da ta gabata babban mai shigar da karar ya aikewa da Firaministan bukatar ganin ya bayyana gaban kotu jiya talata don amsa tambayoyi da ke matsayin kari kan bayyanarsa gaban mahukuntan kasar sa’o’I kalilan bayan kisan shugaba Moise amma kuma yaki mutunta gayyatar.