Masu garkuwa da mutane wadanda aka fi sani da ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wata amarya a kan hanyar kai ta gidan angonta a jihar Neja.
Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a kasar ta ce ‘yan bindigar sun bayyana ne a lokacin da ‘yan uwa da abokan amaryar ke hanyarsu daga kauyen Allawa na karamar hukumar Shiroro zuwa gidan angon nata a garin Fandogari na karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.
Rahotanni sunce maharan da ke da matukar yawa sun yi wa ayarin amaryar kwanton bauna ne a ranar Juma’a a kan hanyarsu, inda suka dauke amaryar. Da sauraan wadanda ke cikin motar.
Wasu majiyoyi sun ce masu garkuwa da mutanen, wadanda suka yi awon gaba da dimbim shanu, sun kuma kai hari a kauyen Gyaramiya a karamar hukumar shiroron har ila yau, inda suka sace dimbim mazauna kauyen.
Kokarin samun kakakin ‘yan sandan jihar don karin bayani ya ci tura.
Ba wannan ne karo na farko da masu garkuwa da mutanen ke karkata akalar amarya a kan hanyarta ta zuwa gidan angonta ba.
A wani labarin na daban kuma ‘Yan bindiga sun kashe akalla mutane 17 a lokacin da suka kai sabon farmaki kan wasu kauyuka da ke kananan hukumomin Wushishi, Lavun da kuma Mashegu a jihar Neja.
Wasu mazauna yankunan da suka tsira sun ce ‘yan bindigar haye kan Babura sun rika afka musu ne daya bayan daya, inda suka kaiwa kauyuka fiye da 20 farmaki tare da sace mutane da dama.
A karamar hukumar Lavun, rahotanni sun ce akalla kauyuka 10 ‘yan ta’addan suka afkawa, 6 a karamar hukumar Mashegu, sai kuma wasu karin kauyukan a karamar hukumar Wushishi.
Sai dai har yanzu babu karin bayan ikan wadannan alkaluma daga hukuma.