Manoman tumatur a Jihar Katsina na kokawa kan yadda za su dawo da kudin da suka zuba a noma, sakamakon faduwar tumatirin a ’yan kwanakin nan.
Manoman tumatur dun sun ce sun kashe makudan kudi wajen sayo injinan ban-ruwa da na kashe kwari da taki da sauransu.
Malam Halliru Sani, wani manomi ne a garin Tafoki da ke Karamar Hukumar Faskari, ya ce, a wannan shekara, abin da suke sa rai shi ne samun kudade masu yawa, inda manoma da dama suka kauce wa noman saboda rashin jari.
“Saboda tsadar man fetur da taki da sauran kayayyakin amfanin gona da yawa daga cikinmu za su gwammace mu je mu hada da noman kabeji.
“Amma duk da haka mun yi noman tumatir bisa tsammanin samun riba mai yawa, amma abin takaici, sakamakon ya saba wa tsammaninmu.
“Farashin da ake samu a kasuwanninmu na cikin gida ba ya da kyau,” in ji Sani.
Ya danganta matsalar da son-kai na dillalan tumatir da sauran dillalai, wadanda a cewarsa, a koyaushe suna hada kai da manoman gida.
“Dillalai sun mamaye kasuwanni, ta yadda manomi ba ya hulda kai-tsaye da masu saye.
“Suna sarrafa kasuwancin ta hanyar sayen amfanin gona da kai shi kasuwa, inda suke samun riba mai yawa.
“Manoman suna samun riba ce kawai a kasuwanni idan amfanin gona ya yi karanci,” in ji shi.
Ya kara da cewa, “Ko a lokacin bikin Sallah da ya gabata sun sayar da kwandon tumatir a kan Naira 3,500 kafin ya koma Naira dubu 2,000.
“Sai dai kuma farashin ya kara daraja kwanaki kadan da suka gabata, inda ake sayar da kwandon a tsakanin Naira 4,000 zuwa Naira 5,000, amma manoma da dama sun yi asarar wani kaso na kudaden shiga.”
Wani manomi a Funtuwa, Malam Shu’aibu Aminu ya ce, ‘‘Da yawa daga cikinmu sun yi asara, bayan mun yi fama da cutar da ta kusan lalata amfanin gonakinmu.
“Baya ga tsadar man fetur da taki, mun fuskanci mummunan hari daga tsutsa, wanda hakan ya sa muka bukaci magungunan kashe kwari masu tsada lokaci zuwa lokaci don rage yaduwarta.
“Idan muka dubi farashin kuma muka kwatanta da farashin kasuwa, sai mu ga mun yi asara. Amma wadanda suka hada shi da kabeji suna da riba a kanmu.”
Ya shawarci manoma dsu daina noman amfanin gona guda daya domin kare dimbin jarin da suke zubawa.
Daya daga cikin dillalan tumatir a garin Danja, Malam Hamza Idris ya ce, manoma a koyaushe suna neman hanyar dora laifin a kan dillalai, musamman idan farashin kasuwa bai yi musu dadi ba.
“Yawancin manomanmu a nan ’yan gida ne da ba za su iya samar da hanya a kasuwa ba tare da taimakonmu ba.
“Wani bangare na aikinmu shi ne hada masu saye daga nesa da kusa da manoma a yankunansu, amma duk lokacin da aka samu raguwar farashin kayan amfanin gona ko kuma sauyin yanayi, manoma za su dora mana laifi.
“Amma idan abubuwa suka yi kyau, ba za su yaba mana ba,” in ji Idris.
Ya kara da cewa, a koyaushe abubuwan bukata da wadata su ne ke tantance farashin kasuwa, kuma a bangaren tumatir da ke lalacewa, babu yadda za a yi dillali ya boye shi ko kuma ya yi amfani da kudinsa.
DUBA NAN: Kwamitin Majalisa Ya Kira Ministan Wuta
Wakilinmu ya lura cewa, tun daga lokacin bikin Sallah, jama’a na jin dadin farashin kayayyaki a kasuwannin cikin gida.