Mali ta amince ta karbi dakarun kiyaye zaman lafiya na majalisar dinkin duniya guda dubu 1 daga Chadi, biyo bayan matakin Faransa na rage nata sojojin a kasar da yaki ya daidaita.
Wannan yarjejeniyar na zuwa ne a daidai lokacin da Faransa ke rage dakarunta a kasar mai yawan al’umma miliyan 19, bayan da ta shiga don taimakawa wajen yakar ta’addanci a shekarar 20213.
A watan Yuni ne shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya sanar da matakin rage dakarun kasarsa a Mali, bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita a watan Agustan 2020.
A wani labarin na daban kuma hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta amince da tura tawagar masu bincike zuwa kasar Habasha mai fama da rikici, a daidai lokacin da masu bibiyar lamurra a kasar ke gargadin yiwuwar kazancewar lamurra kowane lokaci daga yanzu.
Tuni dai kasar Habasha ta yi kakkausan suka kan zaman da kuma kudurin hukumar ta kare hakkin dan adam, inda jakadanta Ambasada Zenebe Kebede ya ce ana amfani da ita ne a matsayin wani makami na matsin lambar na siyasa, da kuma wani sabon salon a mulkin mallaka a zamanance.