Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana sabbin takadun kudin Najeriya da aka sauyawa fasali.
Gwamnan CBN ya mayarwa kungiyar Miyetti Allah da Majalisar dattawa martani kan kara wa’adi.
Nan da ranar 31 ga Junairu, 2023 duk wanda bai kai tsaffin kudin sa banki ba sun zama takarda
Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, a ranar Talata ja jaddada cewa ba zasu tsawaita ranar daina amfani da tsaffin takardun Naira ba.
Emefiele ya bayyana cewa ranar 31 ga Junairu, 2023 ce ranar karshe ta amfani da tsaffin kudin, cewar CBN.
Yayin hira da manema labarai bayan taron MPC na bankin, Emefiele yace:
“A’a, ba zamu kara wa’adi ba, abinda muka yi bai saba doka ba; daidai yake da doka.”
Daga yanzu Za’a Rage Buga N500 da N1000, zamu fi buga N20, N50, N100: CBN
“Mun sanar da wannan shiri tun ranar 26 ga Oktoba, 2022, kuma munce idan sabon kudin ya fito, za’a iya amfani da tsaffin tare da sabbin har zuwa ranar 31 ga Junairu, 2023.”
“Kusan kwanaki 100 kenan, kwanaki 100 sun isa mutum a kowani lungun Najeriya ya kai kudinsa banki kuma ya shirya kwashe kudinsa idan sabbi suka fito.”
Bankin CBN zai rage buga manyan kudade, N20, N50, da N100 zasu fi yawa
Babban bankin Najeriya CBN na shirin rage yawan takardun kudin N200, N500 da N1000 dake yawo cikn al’umma don rage hauhawan tattalin arziki.
Emefiele ya ce ko a kasar Birtaniya, Fam 50 aka fi kashewa, sannan Fam 20, amma a Najeriya ba haka bane.
Ya ce adadin N500 da N1000 dake gari sun fi kananan yawa.
A cewarsa:
“Maganar gaskiya zamu rage adadin N200, N500 da N1000 da ake bugawa da wadanda ke yawo. Mutane su fara amfani da N50.”
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana sabbin takardun Naira da za’a rika amfani da su a Najeriya ‘Naira’ yau
Ya bayyana kudaden ne a taron majalisar FEC ranar Laraba 23 ga Nuwamba, 2023 a fadar shugaban kasa, Aso Rock Villa, Abuja.
Wadanda suka hallara zaman akwai ministoci da gwamnan babban bankin Najeriya CBN.
Hakazalika akwai shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC, Mr AbdulRasheed Bawa.
Source:Legithausa