Ministan kudi na kasar Ghana Kenneth Ofori-Atta, ya ce hadin gwiwar Sin da kasarsa, ya kasance mai matukar muhimmanci ga ci gaban tattalin arzikin kasar ta yammacin Afrika.
Cikin jawabin da ya gabatar da yammacin ranar Talata a wani biki da aka yi albarkacin cika shekaru 74 da kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin, Ofori-Atta ya yabawa kasar Sin bisa dimbin goyon bayanta ga kasar Ghana a dukkan fannonin tattalin arziki, ciki har da taimakawa kasar samun rancen dala biliyan 3 daga asusun bada lamuni na duniya.
Haka kuma, ministan ya ce Ghana ta ci gajiyar hadin gwiwar kasashen biyu a fannonin ababen more rayuwa da ilimi da tsaro da aikin gona da sadarwa da kiwon kifi. (Fa’iza Mustapha)
A bangaren labarin wasanni kuma Napoli ta mayar da martani ga wani faifan bidiyo na TikTok mai cike da cece-kuce akan dan wasanta kuma dan Najeriya, Victor Osimhen.
A wannan makon, an ba da rahoton cewa Osimhen na iya daukar matakin shari’a a kan Napoli saboda wani faifan bidiyo na TikTok wanda yake shagube akan Osimhen saboda ya barar da bugun fanareti yayin karawa da Bologna a wasan Seria A.
Amma, kungiyar ta Serie A a cikin wata sanarwa ta ce ba za ta iya yi wa Osimhen shagube ba, wanda ta ke daraja shi a matsayin dan wasa.
Idan Victor na ganin wannan shagubene akansa to wannan ba shine abin da kulob din ya nufa ba.
Idan zaku tuna Leadership Hausa ta bayyana cewar a ranar Talata da yamma, wakilin Osimhen Calendar ya bayyana cewar zasu dauki matakin shari’a akan kungiyar.
Source LEADERSHIPHAUSA