Farashin gangar man fetur ya sake tashi a kasuwanninsa na duniya a cinikin yammacin ranar jiya Juma’a, inda farashin ya haura sama da dalar Amurka 100 kan ganga guda.
Da karfe 12:43 agogon Moscow, an yi cinikin danyen mai na Amurka a kan farashin dala 94.59 kan gangar guda, wanda ya karu da kashi 0.26% daga farashin rufe kasuwar a yammacin jiya.
A halin da ake ciki, an sayar da danyen mai na Brent a kan dala 100.14 kan gangar man daya, wanda ya karu da kashi 0.54 cikin dari bisa farashin da aka sayar a baya, a cewar rahoton Bloomberg.
A wani labarin na daban a karon farko tun bayan rikicin Rasha da Ukraine, wani jirgin ruwa ya tunkari kasar Ukraine domin dibar tsaba zuwa nahiyar AFrika.
An bayyana jirgin ruwan zai nufi kasar Habasha a karkashin wani shiri da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya na fitar da hatsi daga Ukraine domin shawo kan matsalar abinci a duniya.
Rikicn Rasha da Ukraine manyan kasashe wajen samar da alkama ya sa farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabo a duniya tare da haifar da matsalar karancin abinci a kasashen Afirka da Gabas ta Tsakiya da kuma wasu sassan Asiya.
A karon farko a cikin ‘yan kwanakin nan, jiragen ruwa da yawa masu jigilar hatsi sun bar tashoshin jiragen ruwa na Ukraine a karkashin sabuwar yarjejeniyar, amma yawancin jigilar kayayyaki abinci ne na dabbobi.
A ranar Juma’a, shugaban majalisar Tarayyar Turai Charles Michel ya sanar da cewa nan ba da dadewa ba za a yi lodin kayan agaji na farko da hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta shirya zuwa Afirka, kuma hatsin da za’a kai kasar Habasha, na daga cikinsu.
A karon farko jirgin mai suna Brave Commander, ana sa ran zai dauki fiye da ton 23,000, a cewar ma’aikatar samar da ababen more rayuwa ta kasar Ukraine.
Habasha, tare da Somaliya da ke makwabtaka da Kenya, na fuskantar fari mafi muni cikin shekaru arba’in a yankin kahon Afrika.
Source: ABNA