Manoma sun koka akan rashin samun dauki a fannin noman amfanin gona da suka hada da, Rogo, Doya, Shibkafa da sauran amfanin gona.
Shugaban kungiyar manoman Doya na jihar Edo Luke Osagie ya bayyana hakan a hirarsa da manema labarai a jihar.
Sai dai, Osagie ya sanar da cewa, duk da irin wannan kalubalen da maoman Doyar ke fuskanta a jihar manoman ta a jihar na ci gaba da samun nasarori, musaman wajen samun girbi da dimbin riba mai yawa.
Shugaban ya buga misali da yadda Fulani makiyaya ke shigar masu gonakansu, inda dabbibin su ke cinye masu amfanin gonakan su da suka noma.
“Duk da irin wannan kalubalen da maoman Doyar ke fuskanta a jihar manoman ta a jihar na ci gaba da samun nasarori, musaman wajen samun girbi da dimbin riba mai yawa.”
A cewarsa, akasari muna zama a cikin gonakan mu ko kuma ani jeji da ke a kusa da gonakan domin hana makiyayan shiga cikin gonakan namu.
Ya kara da cewa, idan muka hana su shiga cikin gonakan suna yin fada damu, inda mu kuma muke mayar masu da martani, wasu kuma makiyayan don gudun kar makiyayan su halaka su, suna arce wa su bar gonakan nasu.
“Akasari muna zama a cikin gonakan mu ko kuma ani jeji da ke a kusa da gonakan domin hana makiyayan shiga cikin gonakan namu.”
Shugaban ya kara da cewa, na biyu kuma gwamnatin jihar, ba ta bai wa noman Doyar mahimmancin da ya dace, har da sauran amfanin gona da manoman jihar suke noma wa tare da rashin samar mana da daukin da ya dace.
“Idan muka hana su shiga cikin gonakan suna yin fada damu, inda mu kuma muke mayar masu da martani, wasu kuma makiyayan don gudun kar makiyayan su halaka su, suna arce wa su bar gonakan nasu.”
“Gwamnatin jihar, ba ta bai wa noman Doyar mahimmancin da ya dace, har da sauran amfanin gona da manoman jihar suke noma wa tare da rashin samar mana da daukin da ya dace.”
A cewrsa, hakan ya janyo mutane a jihar, ba su da sha’awar yin noman na Doyar, inda ya bayyana cewa, ana samun dimbin riba a fannin na Noman Doya.
“Hakan ya janyo mutane a jihar, ba su da sha’awar yin noman na Doyar, inda ya bayyana cewa, ana samun dimbin riba a fannin na Noman Doya. ”
A wani labarain kuwa, Kwamishinan ma’aikatar aikin gona na Jihar Kebbi, Barista Attahiru Maccido ya ce, kashi 80 cikin 100 na manoman jihar kananan manoma ne da ke bukatar ilimin zamani domin inganta harkarsu ta noma.
Maccido ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da a ofishinsa a Birnin Kebbi, inda ya shawarci manoman jihar su tashi tsaye wajen yin amfani da kayayyakin zamani domin inganta harkarsu ta noma.
Maccido ya ce noma hanya ce ta yin arziki inda wadansu jama’a suka dauke shi sana’ar wahala, inda ya ce, yanzu kasashen waje sun yi nisa wajen inganta sana’ar noma daga yadda ake yin sa a shekarun baya zuwa na zamani.
A cewarsa, ya zama wajibi manoma su tashi tsaye wajen inganta wannan sana’a tasu, da kuma su daukart fannin a matsayin sana’a domin ta haka ne za su rika bin duk hanyoyin da suka dace wajen inganta noman.
Kwamishina ya kara da cewa, Thailand ce da ta shahara wajen noman shinkafa da samar da abinci a duniya amma kuma abin mamaki, kasar ba ta da rabin kasar noma irin wadda Allah ya ba Nijeriya.
Ya sanar da cewa, saboda yin amfani da bincike da kimiyya yanzu Thailand tana kan gaba wajen samar da abinci ga kasashen duniya mu ma Jihar Kebbi haka muke son mu zama a kan gaba a cikin kasashen duniya masu alfahari da aikin noma.
Ya ce, tun ranar da Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin noma a Jihar Kebbi aikin noma ya farfado saboda ko an mika ragamar aikin noma ga mai kishin kasa da son jama’a su zama masu dogaro da kansu domin samun karin arziki.
Kwamishinan ya ce, gwamnatin Jihar Kebbi tana kokari wajen taimaka wa manoman jihar da dabarun zamani da za su taimaka musu domin inganta noma a fadin jihar.
Ya ce, ko a kwanakin baya gwamnatin jihar ta rarraba wa manoma kudaden tallafin yin noman rani na shekara 2019.
Kwamishinan ya ci gaba da cewa, manoma 8,600 suka samu Naira bashin Naira dubu 150 kowanensu, inda ya kara da cewa, a shekara uku da suka gabata manoman shinkafa dubu 120 suka amfana da tallafin yin noma, sai manoman waken suya dubu biyar da suka amfana da shirin ba da tallafin noma, manoma alkama manoma dubu 1600 gwamnatin jihar ta ba rancen noman alkama.