EFCC ta shirya yin gwanjo da kadarorin wasu ‘yan siyasa da ‘yan kasuwan da aka samu da laifin sata ciki har na Diezani Alison Madueke.
Kadarorin da za a sa a kasuwa su na Legas, Ribas, Abuja, Anambra, Gombe, Ebonyi, Kaduna, dsr.
Mai sha’awar mallakar kayan zai je shafin EFCC ya samu fam, daga nan zai je ya ga kayan da idonsa.
Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa tayi kira ga mutane su nemi sayen kayan da gwamnati ta karbe.
A karshen makon nan Daily Trust ta rahoto cewa kayan da gwamnatin tarayya ta karbe su na garuruwan Legas, Ribas, Anambra, Gombe da Delta.
Har ila yau an karbe kaya daga ‘yan siyasa daga ‘yan kasuwa a jihohin Ebonyi, Kaduna, Delta, Edo, Kwara, Kuros Riba, Osun, Oyo da birnin Abuja.
Ana zargin daga cikin kaya da kadarorin da aka karbe a biranen Abuja, Legas da Fatakwal na tsohuwar Ministar fetur, Diezani Alison-Madueke ce.
Gidaje 23 sun shiga kasuwa Hukumar EFCC ta na tuhumar Diezani Alison-Madueke da mallakar wadannan kaya ta haramtacciyar hanya. Tun 2015 ake shari’a da ‘yar siyasar a kotu.
Rahoton ya nuna a unguwar Banana Island da ke Legas, katafaran gidaje 23 aka karbe a hannun Allison-Madueke wanda tayi Minista a mulkin PDP.
A wani jawabi da ta fitar a ranar Asabar, 25 ga watan Disamba 2022, hukumar EFCC ta ce mutane da kamfanonin da suke sha’awar kayan za su iya sayensu.
Akwai sharadin mallakar kayan Daga sharudan da aka bada shi ne ya zama hukumar ba ta taba samun mutum da laifi ba.
Za a iya samun labarin nan a jaridar Aminiya ta ranar Asabar
Duk wani wanda aka taba daurewa a baya a dalilin aikata laifi, bai cikin wadanda za su samu damar sayen wadannan kadarori da ake shirin yin gwajonsu.
Masu neman ayi masa gwanjon za su iya sauke fam daga shafin yanar gizo na hukumar (watau www.efcc.gov.ng), bayan nan sai su dirje kayayyakin.
Kadarorin nan sun hada da wani gida mai dakuna uku da sashen samari a rukunin gidaje na Foreshore a titin Onikoyi da ke unguwar Ikoyi a jihar Legas.
EFCC v Diezani Alison-Madueke Tun a karshen shekarar bara, aka samu rahoto cewa Gwamnatin tarayya ta fara shirye-shiryen sa kadarori da dukiyoyin wasu ‘yan siyasa a kasuwa.