Taron Davos na lokacin zafi da ake gudanarwa a birnin Tianjin na kasar Sin, ya samu halartar mutane sama da 1,500 daga bangarorin siyasa, da kasuwanci da ilimi daga kasashe da yankuna kusan 100.
Babban jigon na bana dai shi ne “Kasuwanci: Ƙarfin dake raya tattalin arzikin duniya”, da sake shirya samun ci gaba” a matsayin daya daga cikin muhimman jigoginsa, wanda ke nuna sha’awar mutane.
Idan har ana son samun ci gaba, dole ne mutum ya samu kuzari.
Kuma daga ina za a samu wannan yunkuri?
A matsayinta na kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, kuma kasar dake kan gaba a duniya a fannin cinikayyar kayayyaki tsawon shekaru shida a jere, bisa dabi’a kasar Sin ta zama wani muhimmin abin da ya fi daukar hankali.
A cikin shekaru 10 da suka wuce, matsakaicin ci gaban tattalin arzikin kasar Sin a shekara, ya kai kashi 6.2 bisa dari, wanda ya ba da gudummawar sama da kashi 30 cikin 100 ga ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya, abin da ke zama injin mafi girma wajen bunkasa tattalin arzikin duniya.
Ga masana’antun duniya kuwa, kasar Sin ba wai “kyakkyawan labarin bunkasuwarta” ba, har ma da damar da take samarwa ta samun nasara tare. A shekarar 2019, Alex Zhavoronkov ya mayar da hedkwatar kamfaninsa zuwa kasar Sin, saboda fifikon da yake da shi a fannin manyan hazaka na fasaha da kuma ’yancin cin gajiyar nasarorin binciken kimiyya da ake da su.
Daga gudanar da mu’amalar tattalin arziki da cinikayya zuwa inganta hadin gwiwa a fannin fasaha, zuwa neman “hadin gwiwa”, da yawan kamfanonin duniya suna mai da hankalinsu ga kasar Sin. (Ibrahim Yaya).