Majalisar Dattawa ta sahale wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ciyo bashin Dala miliyan 500 da nufin samar da mitocin wutar lantarki ga ’yan Najeriya
A zaman majalisar na ranar Labara ne ta amince wa Shugaba Bola Tinubu ya karbo bashin daga Bankin Duniya.
Bayan karbar rahoton kwamitin basukan kasashen waje ne majalisar ta amince da karbo bashin wanda za a damka ga Hukumar Kula da Kamfanonin Gwamnati (BPE).
Bashin Dala miliyan 500 da za a sayi mitocin lantarkin da su wani bangare ne na bashin Bankin Duniya na Dala biliyan 7.94 da Tinubu ya samu anincewar majalisar da zai karbo a karkashin tsarin karbar basukan kasashen waje na 2022-2024.
Da yake gabatar da rahoton, mataimakin shugaban kwamitin, Sanata Haruna Manu, ya ce kudaden da mitocin za su taimaka wajen ingata samun wutar lantarki a kasar.
A cewarsa, aikin samar da mitocin zai kara ingantar karfin kamfanonin rarraba wutar lantarki da kuma samun kudaden shiga a gare su.
A wani labarin na daban kungiyar Ƙwadago NLC ta yi fatali da tayin naira 48,000 da Gwamnatin Tarayya ta gabatar a matsayin mafi ƙarancin albashin ma’aikata a ƙasar
Mambobin ƙungiyar ta NLC a wannan Larabar su bayyana mamakin dalilin da gwamnati da mambobin kamfanoni masu zaman kansu ke tozarta su da abin da ta bayyana a matsayin tayi mai ban dariya.
Aminiya ta ruwaito cewa a yayin da Gwamnatin Tarayya ta miƙa tayin Naira 48,000, ‘yan ƙungiyoyi masu zaman kansu sun miƙa tayin N54,000.
DUBA NAN :Babbar Kotu Ta Dakatar Da Kama Tsohon Gwamna Ganduje
Sai dai ƙungiyar NLCn ta bayyana adawartwa kan duk tayin da ɓangarorin biyu suka gabatar a wani taron tattaunawa da aka gudanar a babban Ofishin NLC na Labour House da ke Abuja.