Malami a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, kuma mai sharhi a kan al’amurran yau da kullum, FARFESA SALIHU ADAMU DADARI ya rabe tsaki da tsakuwa game da dokar ta bacin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana a kan bangaren samar da abinci a kasar nan. Farfesan ya yi bayani a kan yadda za a iya samun nasarar dokar da matsalolin da za su iya haifar da cikas ga shirin. Ga dai yadda hirarsu ta kasance da Mataimakin Edatanmu, BELLO HAMZA:
Za mu so ka gabatar mana da kanka…
Suna na Farfesa Salihu Adamu Dadari na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, tsangayar aikin gona a fannin koyar da binciken noma da dabarunsu (IAR). Kuma mai tsokaci a kan al’amuran yau da kullum a duniya baki daya.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya dokar ta-baci a kan harkar samar da abinci; me wannan doka ke nufi?
Ita wannan doka ta shafi shigo da abinci daga wadansu kasashen waje. Saboda idan an shigo da abinci daga wata kasa yana tauye arzikin kasar Nijeriya. Kuma abincin da manoman mu suke haba-haban nomawa zai yi kasa kwarai da gaske.
Domin haka ka ga wanda a da aka dakatar, manoma sun dan wargaje. Sun samu nasara. Sai dai inda aka samu kuskure da aka zo da canjin kudi wadansu sun dunga kabar da abincinsu yanzu ga hau ta hau su. Domin su ma suna jinta a jika. Shi yasa muke son shugaban kasa ya rika daukar mutane kwararru a kan fannoninsu.
Kamar ministan gona ya kasance wanda ya karanta gona ya kware. Ministan lafiya ya zama likitan da ya goge a kan fannin lafiya. Wadannan wurare guda biyu idan ka bar su suka tagayyara a wurin ‘yan siyasa, to kasa za ta mutu murus.
Shi yasa ka ga Nijeriya yanzu tana kwan-gaba kwan-baya.
Abin da ake so wa Nijeriya ta yi, idan ka ba da irin wannan doka, to ka sawwaka wa manoma farashin takin zamani, magungunan kwari da kuma iri mai nagarta su same shi a sauki. Kuma wadatacce. Idan Allah ya kawo ruwa mai nagarta, za ka ga abinci ya yawaita kuma komai ya tafi cikin tsari. Kuma tattalin arzikin kasa zai bunkasa a cikin kankanin lokaci. To amma wannan bai taba tabbata sai da zaman lafiya.
Yanzu ka ga kasarnan dai an dabaibaye ta da masu garkuwa da jama’a, ‘yan Boko Haram, ‘yan ISWAP, da ‘yan gani kashe ni. To ba yadda za a yi kasa za ta ma ci gaba. Ba sai ka samu damar zuwa gona ba? Sannan za ka iya zuwa?
Yanzu Nijeriya tana da murabbu’in eka mil miliyan dari na noma wanda kasa ce wadatacce, amma a yanzu abin da ake nomawa ake amfani da shi bai kai murabbu’in mil miliyan ashirin da biyar ba. Ka gani mil miliyan saba’in da biyar daji ne, kamar ka tashi zuwa Kaduna zuwa Birnin Gwari, ka ga daji ne kake gani ba wani gona.
Haka inka tashi daga Kaduna zuwa Abuja daga nan na wuce zuwa su Akure, ka ga daji ne. Duk inda gari yake ana noma. To ka ga Allah ya yi mana albarkar fili wadatacce, wanda idan aka inganta noma za a ci gaba, to an ki. Saboda haka kowa ya rike bironsa ya zauna a ofis. Sai ‘yan kasuwa masu gudun hijira, masu noman abin da kawai a saya su boye su ajiye su ci riba.
Wato imanin dan Nijeriya ya raunana, to ka ga wannan bai taba tabbata sai mun koma ga Allah. ka ga dai akwai Fastoci akwai Limamai ana wa’azi amma duk ba ya shiga.
Ka rika lura fa, ba wai ina sukarsu ba ne, ka lura duk wani fitina na hauhawar kaya da rufa asiri na boye kaya, a arewa yake. Kuma arewar nan idan ka duba za ka ga yawanci mutane ne wanda suke cewa suna tare da Allah. Ka duba fetur yadda aka raba shi. Mutanenmu ke boye fetur, mutanenmu ke tallatawa ya yi tsada. To haka abincin, wani ya saya ya tara ya boye. Yanzu da ya kai dubu arba’in buhu kaza, su suke fitowa da shi suna sayarwa. Ka ga babu tausayi babu tausayawa. Ba yadda za a yi kasa za ta ci gaba da irin wannan badakalar bala’in.
To ta yaya talaka zai amfana da dokar ta-baci da gwamnati ta sa a kan samar da abinci?
Shi ba zai fahimta ba, saboda ya riga ya bi inna rididi. Manya da za su yi adalci sun cuce shi, shima ya ce to a yi ta cutar. Idan ka je ma’auna za ka ga, ka kai masararka za a auna da babban tiya idan ka koma ka saya sai ka ga karami ne. Ka ga talaka ya fada ciki. Talaka na cutar talaka. Ai tunda kasar ta riga ta dimauta, sai dai addu’a. Amma babbar nasara, da ana hukumci mai tsanani, to da an samu gyara.
Za ka ga lauya na wasa da hankalin jama’a domin ya samu kudi kuma a karya. Za ka ga Alkali ya karbi cin hanci ya ki yin shari’ar yadda ya dace.
Kana ji nan Bulkachuwa dan majalisar Dattijai da ya sauka ya ce matarsa ma ya kan kai mata mutane ita ma ta yi musu gudummawa. Ka ga ba kasar da za ta ci gaba ba doka ba oda. A Nijeriya ka rika lura, za ka ga an kai da kai ko da ‘particulars’ ka manta idan ma ba ka manta ba, ana kokarin ka manta a karbi kudinka.
Ana son a bi doka da oda, ga shi ba zaman lafiya. Inda ake noma, an tarwatsa mutane; kamar wajen su Zamfara din nan, su Katsina, su Birnin Gwari, Dan Sadau, du wurare da dama a Sakkwato, ka ga dan noman da ake yi, ka ga ya ragu. Abinci inda za a noma shi ya karanta.
Ana ganin rashin sa ido a kan hauhawar farashi ya sabbba tsadar farashin abinci a Nijeriya, me zaka ce a kan haka?
Ai ko ta sa dokar ba zai yi aiki ba. Don ba a hukunci, da ana hukunci, to idan ta sa dokar za a yi. Amma ba hukunci. Saboda haka idan kana da uwa a murhu ko kana da kudadenka kai kake da gaskiya. To ka ga kasar inda ta kai wannan marhalin, to sai dai addu’a. Shi yasa muka cewa a riaa yi wa shugabannin addu’a na alheri. Ba a dunga kunduma musu ashar ba.
A rika musu addu’a, Allah ya ba su hikima da basira da fahimtar yadda za su ci gaba da raya kasar ta samu dawwama mai alheri.
Farfesa wasu na ganin cewa tunda an kafa dokar ta-baci ya kamata a ce a bude iyakokin Nijeriya a yi ta shigo da abinci, kuma a bai wa mutane daban-daban lasisin shigo da abincin domin ya wadata?
To, amma ai kuma tattalin arzikinmu zai rushe, saboda abincin da ake shigowa da shi ai ba kyauta ba ne. Ka ga komai arharsa kai da ka yi naka za ka sayar, ka ga naka na daya, ba za ka mayar da kudin da ka noma ba. Na biyu; masu noman za su ragu domin sun ga babu riba. To abin da ake so da gwamnatinmu tana tafiya da tsari, a kasar Malawi akwai shugaba da aka yi, Dakta Hastings Banda, lokacin yana minista ne na gona, to shi kafa doka ya yi, ya samu daurin gindin shugaban kasa a lokacin. Idan za a yi noma kamar na bana din nan an riga an yi lissafin abin da za a kashe a hekta, an kiyasta ga abin da za a samu, komai yana tafiya daidai, akwai ruwa mai wadata, akwai yanayin rana da takin zamani na maganin kwari, sai su bada kudi na bashin shekara mai zuwa. Kowanne buhu tan kaza za a saya kaza, to idan lokaci ya yi, haka za a saya. Sai a sa shugabannin a kasuwa, ba cin hanci, haka za ka saya. Idan ya ragu ya yi rara, gwamnati ta tara ta ajiye a rumbun hatsi ko rumbun ajiya. To lokacin da aka samu nakasu na abinci ya gaza, to sai a fito da shi gwamnati ta san yadda ta saya wurin manoma ba riba. Domin ta daidaita sahu. To haka suke bajet, idan an zo bajet shugaban kasa zai fada, idan ka noma kaza ka ga farashinsa, idan ka nomi kaza ga farashinsa, to haka suka rika tafiya har aka wayi gari har ya zama shugaban kasa. To haka kasar ta ci gaba.
To ban san yanzu ba, ka san kowanne zamani da na shi al’amari. To Nijeriya idan misalin mun samu shugaba na kwarai ya yi misalin, to wani juyin idan ba mu samu mai wannan Shirin ba da’ar ba, to gaba daya sai abin ya tarwatse.
To Nijeriya dai ita ko da ana samun shugabanni, ka rika lura wadanda aka yi da su bariya da bara wancan suke shiga gwamnatin su kawo ‘ya’yansu su kawo na gaba da su ‘yan goshinsu, abin ya zama kasuwanci. Ka ga kuwa shugabanci, kudinka da ka kashe shi za a baka ka mayar kuma ka ci riba, za ka ga ya zama kasuwar shinko, to duk gwamnatin da ta zama kasuwar shinko, ai ka ga ba ci gaba a nan. Taro ne kamar na ‘yan damfara haka. To mu dai Allah ya ci gaba, ya kiyaye, Allah ya kyauta.
Mu ci gaba da yi ma shugabannin addu’a. Allah ya ba su hikima, ya ba su basira, su dubi ‘yan Nijeriya. Mu kuma ‘yan Nijeriya, Allah ya daidaita al’amarinmu mu yi tunani mai kyau mai nagarta. Na biyu; imani da yakini da yarda da Ubangiji don kasar ta ci gaba.
Farfesa wani shawara kake da shi ga su jihohi su ma tunda kowanne yana da shi kasafin yana da tsarin, a kan su fuskancin abin da ya shafi harkar gona da samar da abinci?
To ka ga yadda ya kamata daga gwamnatin tarayya za a faro abin har zuwa kananan hukumomi. Kamar yadda na fada maka din a rika tallafawa, a kuma sa matakan tsaro. Ka san wani ma ba ya noma, sai ya je ya amshi kudin ya je ya yi wani hidimarsa da shi. To wanda suke noman ba a ba su. Sai wanda yake da uwa a murhu. To ka ga ba a ci gaba a haka. Kuma siyasar Nijeriya ta dada talauta Nijeriya, domin ba yadda za a yi ana biyan ‘yan majalisu cikakkun kudi na tashin hankali, ya kamata tunda kasar ta tarwatse a wajen tattalin arziki, da an yi ‘parliamentary system’ tunda idan ka zauna, duk ‘meeting’ din da aka yi a ba su na su na su guzurin, amma ba albashi ba, to ka ga da ya rage fada da dambe da kisan kai saboda ka san idan ka tafi duk alawus za a baka. Amma yanzu ya zama kasuwa, yawan zuwanka, yawan kudin da za a baka ka yi ‘project’ ka cinye ka yi kaza. Ka ji fa yadda abin yake tafe. To, a wannan hali idan ba an canja rawa ba, to Nijeriya kullum za ta dulmiya cikin bashi, kuma ‘already’ mun koma koma hannun nasara. Wato gwara 1960 fa, ka ga 1960 ana lallaba mu ne, ana tausayinmu, to yanzu tunda suka gane mun waye mun san komai, to buge mu ake yi kai tsaye, kuma da ‘yan Nijeriya ake wannan. Ka ga kasarnan tana da ma’adinai masu yawan gaske, kowanne kauye idan ka je. Sa’annan tana da albarkatun ruwa na albarka da kasa mai nagarta da abubuwa na jindadi, ga yanayi wanda zai rike dabbobi; shanu, awaki da komai wanda ba sai mun nema daga wata kasa ba. Ka ga da ana tafiyar da abu bisa tsari, ba sai mun je mun saya abinci a Thailand ba, ko a kasar Amurka, ko inda ake yakin nan na Ukraine. Ka ga Ukraine ba ta kai jihar Kaduna ba amma ka dubi yadda ake bala’in cewa ta tsaya ana yaki ba a samu Alkama ba, ba a samu kaza ba.
Alkamar nan za mu iya yinta ‘within sabannah’ tun daga gefen Gwoza din nan zuwa su Gombe, su Adamawa, su Kano, zuwa su Talatan Mafara, har iya Rima a Sakkwato. Ka ga ba za mu iya cinye Alkamar ba idan da za mu yi.
To, amma ka ga mun sa kanmu sai dai mu je mu saya. Wannan bala’i ne, da rashin adalci da rashin tunani. Shugabanninmu da za su natsu da yardar Allah, akwai mu da matsaloli da yawa wadanda ba su da iyaka. Yanzu za su cika littattafai na tarihi da da ban mamaki. To kasar tana son jajirtattun shugabanni masu imani, masu tausayi masu yakini, masu maganin ko ta kwana, to kasa za ta gyaru.
To a takaice Farfesa, shi wannan shiri na dokar ta-baci da shugaban kasa ya sa a bangaren samar da abinci, menene nasara da rashin samun nasarar tsari?
To wannan tsarin dai mu muna fata shugaban kasa ya bi tsarin kamar yadda ya yi masa tanadin alheri, ya bi shi da abubuwan da suka kamata, ya tabbatar dokar ta tafi daidai.
Babu nakasu ba magudi. Masu aiwatar da shi su bi shi sau da kafa. Mu inganta noman mu na kasa, a tabbatar bodojinmu, ka san ‘yan Kwastan ma ana sayensu, suna da hanyoyin da za a shigo da abinci kala-kala a mashin. Za ka ga idan ka je wajen su Daura din nan da Kwangalam, gaban Kwangalam ma zuwa wurin Jihar Jigawa, nan suke shiga a daji da mashin, za ka ga mashin sama da dubu kowanne yana daure da buhunan, saboda haka wadannan abubuwa sai mun yi wa kanmu nashiha.
Zan iya cewa kudi suke nema, kuma wannan kudi ba wanda zai tafi da sisin kobo a lahira.
To shiyasa na ce maka musiba ne kudi, sai dai ka roki Allah ya raba ka da bala’in son kudi. Ya ba ka mai amfani mai albarka. To ko da ya yi ma yawa ka taimaka wa al’ummar Nijeriya.
Farfesa mun gode kwarai da gaske.
Nima na gode.