Wasu mata, a yau Litinin sun fito kan titi tare da yin cincirindo a kan titin Kpagungu da ke Minna-Bida cikin babban birnin jihar Neja, inda suke gudanar da zanga-zangar kokawa kan halin matsi da yunwa da tsadar rayuwa da suke fama da shi.
Matan dauke da alluna da aka rubuta “Ba abinci, yunwa na kashe mu” sun bukaci a samar musu da ingantacciyar rayuwa tare da ke lalubo musu magita kan tsadar rayuwa da ta addabe su.
Sun zargi masu rike da mukaman siyasa da rashin kula da halin da suke ciki tare da ke koka wa da rashin samun damar cin abinci koda sau daya a rana.
A wani labarin na daban an ayyana Mista Daniel Asama na jam’iyyar Labour Party (LP), a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Jos ta Arewa/Bassa a tarayya da aka yi ranar Asabar.
Baturen zaben na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa James Damen, ne ya bayyana sakamakon zaben da safiyar ranar Litinin.
Damen ya ce Asama ya samu kuri’u 66,422 inda ya kayar da abokin hamayyarsa Adam Alkali na jam’iyyar PRP, wanda ya samu kuri’u 61,670.
Baturen zaben ya bayyana Ibrahim Hassan na jam’iyyar APC ya zo na uku da kuri’u 10,063.
Damen ya ce “Bayan samun kuri’u mafi inganci da aka kada da cika sharuddan doka, an ayyana Mista Daniel Asama a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Jos ta Arewa/Bassa a zaben Cike-gurbi,” in ji Damen.
Sakamakon, kamar yadda Baturen zaben ya sanar, ya nuna cewa Asama ya yi nasara a karamar hukumar Bassa ta jihar, yayin da Alkali ya yi nasara a karamar hukumar Jos ta Arewa.
Source: LEADERSHIPHAUSA