A yau Alhamis 26 ga wata bisa agogon Geneva, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice, da hukumar kula da ikon mallakar fasaha ta duniya wato WIPO, sun rattaba hannu kan takardar neman yin hadin gwiwa a birnin Geneva na kasar Switzerland, inda bangarorin biyu za su yi hadin gwiwa wajen karfafa ba da kariya da fadakar da ikon mallakar fasaha, da gudanar da ayyukan musaya tsakanin kasa da kasa da dai sauransu.
Mataimakin shugaban sashin fadakar da al’umma na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaban CMG Shen Haixiong da darakta janar na hukumar WIPO Daren Tang ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a madadin bangarorin biyu.
Jakada Chen Xu, zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake kasar Switzerland, ya halarci bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
A wani labarin na daban shugaban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar (CMG) Shen Haixiong, ya tattuna da Klaus Schwab, shugaban dandalin tattauna tattalin arzikin duniya, a Geneva na Switzerland. Bangarorin biyu sun tattauna game da yadda za su ci gajiyar damarmakin da suke da su da kuma ci gaba da zurfafa hadin gwiwa a tsakaninsu.
Shen Haixiong ya ce CMG ta shafe shekaru da dama tana watsa tarukan dandalin, kuma ba tare da fashi ba. Yana mai cewa, bangarorin biyu na da dimbin damarmakin hadin gwiwa.
Ya ce ta hanyar hada hannu wajen gudanar da tsare-tsare da shirya tarukan kafafen yada labarai, da shiga ayyukan gudanar da tarukan dandalin tattauna tattalin arzikin duniya na shekara-shekara, bangarorin biyu sun gabatar da muhimman batutuwan tattalin arziki da bayyana muryoyi daban-daban na duniya da kuma ingiza gina al’umma mai makoma ta bai daya ga bil adama.
A nasa bangare, Klaus Schwab ya bayyana matukar godiya da yadda CMG ke watsa tarukan dandalin tattauna tattalin arzikin duniya.
Ya ce CMG na gabatar da sahihan hiraraki da rahotannin bisa kwarewa da tsare gaskiya da sauke hakkin dake wuyanta a matsayinta na kafar yada labarai ta kasa da kasa. Ya ce suna sa ran hada hannu da CMG wajen amfanin da tasirinsu daban-daban domin karfafa tattaunawa da hadin gwiwa kan batutuwan da suka shafi ci gaban duniya da hadin gwiwar kasa da kasa da damarmakin da kirkirarriyar basira ta kawo da inganta fahimta da aminci da kuma kara sabon kuzari ga ci gaban tattalin arzikin duniya. (Fa’iza Mustapha)
Source LEADERSHIPHAUSA