Hon. Gudaji Kazaure ya fallasa adadin kudin cin hanci da ke cikin kasafin kudin babban bankin Najeriya.
A wata hira da aka yi da shi, Gudaji Kazaure ya tono abin da yake ganin badakala ce a bankin CBN.
‘Dan majalisar ya ce har mafi yawan abokan aikinsa a Majalisa ba su da masaniyar dawar garin.
A wata hira da aka yi da Muhammad Gudaji Kazaure a ranar Lahadi, ‘dan majalisar wakilan tarayyar ya jefi bankin CBN da laifuffuka da da-dama.
Muhammad Gudaji Kazaure ya halarci shirin fashin baki da Waziri Bulama Bukarti suke shiryawa, ya yi bayani kan kwamitinsu da ke binciken badakalar kudi.
‘Dan majalisar na jihar Jigawa ya zargi Gwamnan babban banki da yin kutun-kutun wajen ganin ‘dan jiharsa ya zama shugaban kwamitin kudi a majalisar wakilai.
A dalilin wannan abin da Godwin Emefiele ya yi, Hon. Gudaji Kazaure ya ce ‘yan majalisa ba su iya binciken gwamnan da babban bankin duk barnar da ake yi.
‘Dan siyasar ya shaidawa shirin fashin baki cewa Godwin Emefiele ya saye duk manyan kasar nan.
CBN ya na ba manyan bashin Biliyoyi Daga cikin hanyoyin da ake bi wajen rufe bakin masu mulki, Kazaure ya ce bankin CBN yana bada bashin da ya kai N2bn ba tare da an karbi kadarar mutum ba.
Shi karon kan shi, ‘dan majalisar ya ce an yi masa tayin N1.8bn amma ya ki karba saboda tsoron kashe kudin, yace da ya karbi bashin nan da yanzu an saye shi.
Legit.ng Hausa ta ji Kazaure a hirar da aka yi da shi yana cewa ya san duk wani jami’i, gwamnati ko daidaikun mutanen da bankin CBN ya ba aron makudan kudi.
Daga N500bn a shekarun baya, sai da kasafin kudin CBN ya koma N1.3tr a shekarar 2022, yanzu kuwa Gudaji Kazaure ya ce bankin zai kashe N2.4tr a shekarar nan.
Yadda aka tilastawa Mukhtar Betara Shugaban kwamitin kasafin kudi, Mukhtar Betara ya yi kokarin binciken kudin da ake warewa babban bankin, amma a cewar Kazaure, shugabanni suka tursasa shi.
Gudaji Kazaure yake cewa shi ma ya san da wannan labari ne saboda yana cikin kwamitin, ya ce ‘yan majalisar da ke masaniyar wannan a majalisa ba su kai 40 ba.
‘Dan majalisar ya ji labarin rikici ya barke tsakanin ‘yan kwamitin bayan shugabansu ya karbi cin hancin N1bn daga hannun gwamnan CBN, sai ya raba masu N10m.
Manyan masu kudin Najeriya sun yi gaba An ji labarin cewa, wani rahoto na Oxfam ya nuna a cikin shekaru biyu zuwa uku, kusan 70% na kudin da suka shigo Najeriya sun kare ne a aljihun mutane 83.
Bincike ya nuna a duk ranar Allah, arzikin Attajiran Duniya yana karuwa da fiye da Naira Tiriliyan 1.2, a daidai lokacin da dubunnai suke neman abin da za su ci.
Source:LegitHausa