A kwanaki ne wata kungiya mai zaman kanta mai suna ‘Centre for the Promotion of Pribate Enterprise (CPPE)’ ta aika wa sabon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, (CBN), Michael Olayemi Cardoso, wasika inda ta zayyana wasu matakai guda 10 da ya kamata a dauka da gaggawa in har ana son a dawo da tattalin arzikin kasa a hayyacinsa.
A daidai lokacin da yake shiga ofis a mastayin shugaban Babban Bankin Nijeriya zai fuskanci matsaloli da dama da suke addabar tattalin arzikin kasa wadanda suka hada da hauhawar farashi, hauhawar kudin ruwa, karyewar darajar bankuna, karyewar darajar naira, sune kuma za su zama masa gwaji na farko da zai fuskanta a matsayinsa na jagoran Babban Bankin Nijeriya. Babu wani kokwanto na cewa, lallai Cardoso ya cancanci zama shugaban babban banki musammna ganin irin kwarewar da yake da shi a bangaren ayyukan da suka shafi tattalin arzik a baya.
Hanyar farko da ya kamata ya dauka na fuskantar wadanna matsaloli shi ne, kamar yadda kungiyar ta bayyana, ya sake fasalin bangaren bankunan kasar nan, wannan a cewar su yana da muhimmanci, don shi ne zai dawo da karfin gwiwar masu zuba jari wanda hakan kuma zai taimaka wajen daga darajar Naira da take ta fadi kasa warwas ‘yan shekarun nan. Sake fasalin Naira da tsohon gwamnan babban banki, Godwin Emeifele ya aiwatar ya haifar da matsaloli da dama, ya kuma kamata a gaggauta daukar matakin dakile matsalolin da hakan ya haifar ga bunkasar tattalin arzikin Nijeriya.
Sauran matsalolin sun kuma hada da duba wa’adin shugabancin bankuna da kuma irin kudaden da ya kamata su mallaka na jari don gudanar da ayyukansu, da kuma bukatar nemo hanyoyin hada kai da manyan kamfanonin kasa da na kasashen waje don bunkasa bangaren bankunan Nijeriya.
Yana kuma da matukar muhimmanci a fahinci cewa, Cardoso ya dare karagar jagorancin Babban Bankin Nijeriya ne a daidai wani lokaci mai muhimmanci a tarihin tattalin arzikin kasa. Ba sai mun fada ba, akwai rudani mai girma a bangaren musayar kudaden waje a kasar nan, abin da ya haifar da gagrumin karyewar darajar Naira a kasuwannin duniya. Haka kuma bangaren tattalin arzikin kasa na fama karyewar darajar naira wanda hakan kuma ya haifar da hauhawar farashin albarkatun Man Fetur da na kayan masarufi da ake amfani dasu yau da kullum, akwai kuma bukatar gaggawa na karfafa yadda ake biyan Ruwan basukan da ke bin Nijeriya.
Bangaren harkokin kula da tattalin arzikin kasa sun girgiza da manufofin da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya bullo da su, a saboda haka ya zama doke shugaban Babban Bankin Nijeriya ya samar da wasu manufofi da za su kwantar wa masu zuba jari na ciki da wajen kasa hankali don su ci gaba da hulda da Nijeriya ba tare da wata fargaba ba, ta hanyar daukar matakin farfado da darajar Naira da kuma rage kudaden ruwa a basukan da ake ba masu kanana da matsakaitan masana’antu.
Haka kuma, akwai bukatar shugabannin babban banki a karkashin jagorancin sabbon shugabansu su duba bangaren shiga da fitar da kayayyaki a kasar nan don samar da yanayin da bankuna za su shigo don samar da kudade ga masu kasuwanci a ciki da wajen kasar nan a cikin sauki ba tare da ruwa mai tsanani ba, ta wannan hanyar naira za ta samar wa kanta daraja a fagen kasuwannin duniya.
Ya kamata a dauki darasi daga kamfanonin jiragen sama a kasar nan inda a halin yanzu suke duba wasu bangarori na tattalin arziki don tattabatar da wanzuwarsu a fagen gwagwarmayar kasuwanci, a kan haka bangaren tattalin arzaiki masu zaman kansu suka yi kira ga gwamnati da ta waiwayi wannan bangarn don a karfafa zuciyar masu zuba jari na ciki da kasashen waje.
Shugaban kungiyar da ta yi wannan bincike tare da bayar da wadanna shawarwarin, Dakta Muda Yusuf, ya kara bayar da haske, inda ya bayyana cewa, akwai bukatar a kara daga kudin jari bankuna daga Naira biliyan 2 zuwa Naira Biliyan 25, yana mai cewa, tun shekarar 2004 aka yi wa jarin da bankuna ke amfani da shi kwaskwarima, matsalar da aka fuskanta kuma yana faruwa ne saboda faduwar darajar naira a kasuwannin duniya.
A kan haka, kara darajar jarin bankuna yana da matukar muhimmanci saboda karin jari ga bankuna zai daidata harkokin bankuna da tattalin arzikin kasa, haka kuma kungiyar ta nemi a dakatar da shirin sake wa naira fasali gaba daya saboda babu wani kwakkwarar dalilin yin haka tun da farko.
Haka kuma kafin wannan lokacin, masu manyan masana’antu a kasar nan sun nemi a kawo musu dauki ta hanyar rage ruwan da ake karba a bankuna na basukan da suke karbar don bunkasa harkokinsu, wannan zai karfafa kokarin da gwamnati take yi na mayar da hankali ga wasu bangarori da ba na albarkatun mai ba wajen samo wa kasa kudaden shiga.
Masana na da ra’ayin cewa, gibin da ke tsakanin kudin ruwan da ake karba da kudin da ake ajiiyewa a bankuna yana da fadin gaske wanda hakan yana nuna irin matsalar da ake fuskanta kenan a bangaren harkokin bankunan kasar nan. A kan haka suka yi kira ga sabon gwamna babban bankin ya gaggauta daukan matakin daidaita wannan gibin don samar da ci gaban da ake bukata a bangaren kanana da matsaikaitan masana’antun Nijeriya.
A ra’ayinmu kuma, ya kamata Cardoso ya dauki matakin ceto bangaren kamfanoni masu zaman kansu, daga dukkan alamu yanayin da ake ciki bai basu daman walwala da bunkasa yadda ya kamata ba.
Ganin irin dimbin sanin makaman aiki na sabon Shugaban Babban Bankin Nijeriya, Cardoso, da kuma irin bayanan da ya yi a gaban majalisar dattawa a yayin da ake tantance shi, muna da kwarin gwiwar cewa, za a samu canjin da ake bukkata na kai Babban Bankin Nijeriya matsayin da ya dace da shi, a kan haka muke yi masa fatan alhairi a kan wannan gagarumin aikin da zai fuskanta a shekaru masu zuwa.
Source LEADERSHIPHAUSA