Bankunan Najeriya sun tura sakwanni ga kwastominsu game da wa’adin dawo da tsoffin kudin Najeriya.
Bankin Eco ya wuce iyaka ta kula da kwastoma, inda ya kara adadin kudaden ruwa da kwastomomi za su samu daga ajiye kudaden su.
Gwamnatin Buhari ta hanyar CBN ta samar da sabbin kudaden da za su maye tsoffi; N200, N500 da N1,000.
Bankunan kasuwanci a Najeriya sun fara kira ga kwastomominsu da su tabbatar da dawo da tsoffin kudi zuwa banki.
Wannan na zuwa ne yayin da wa’adin da gwamnati ta sha’anta ke kara gabatowa nan ba da dadewa ba.
A cewar bankunan, rashin dawo da tsoffin kudaden banki zai taimakawa kwastomomi wajen tafka asara da kuma bin dogon layi lokacin da wa’adin ya cika.
Babban bakin Najeriya ya ba ‘yan Najeriya wa’adi, ya ce kowa ya dawo da tsoffin kudi nan da ranar 31 ga watan Janairun bana.
Sakon da bankin Eco ya aikawa kwastomomi
A wani sakon imel da bankin Eco a Najeriya ya aikewa kwastomominsa, ya bukaci su gaggauta kawo tsoffin kudade su ajiye don gujewa tafka asara da bin dogon layi.
Bankin ya kuma tabbatarwa kwastomominsa cewa, za su samu akalla 8% na kudin ruwa daga abin da suka ajiye, rahoton Business Day.
Bankin na Eco ya kuma shaida cewa, tuni ya shirya hanyoyi masu sauki a dukkan cibiyoyinsa domin tabbatar da kwastomomi basu bi dogon layi ba. Shugaban bankin,
David Isiavwe ya kuma shaidawa manema labarai cewa, bankin Eco ba zai karbi ko kobo ba daga wajen kastomomin da ke da sha’awar ajiye tsoffin kudadensu.
Sakon First Bank ga kwastomominsa Bankin ya aikewa da kwastomominsa da sakon tuni ga ajiye tsoffin kudade a banki.
Bankin ya bayyana cewa, zai ci gaba da budewa har ranakun Asabar daga misalin karfe 10 na safe zuwa 1 na rana domin ba kwastomomi damar ajiye kudadensu.
Har yanzu ‘yan NAjeriya basu gama fahimtar batun sabbin Naira ba, da takaita yawan kudi.
Wakilin Legit.ng Hausa ya tattauna da wani mai sana’ar hada-hadar kudi ta POS, ya ce har yanzu wasu mutane basu fahimci ya abin ya yake ba.
A cewar Muhammad Adamu Nasir: “Da yawan mutane kan same ni game da batun kudi, sukan nemi na sauya musu kudin da suka zo dashi, watakila ma asusu wani ya yi, amma abin da yake bukata kawai a sauya masa kudin ya je ya ci gaba da ajiyewa.
“Galibi abin da ba a gane ba har yanzu shine, kawai a zaton wasu an sauya kudi ne, kowa ya kawo a sauya masa ya ci gaba da ajiya.
“Ina kira ga gwamnati da ta krkiri shiri na gidan talabijin ko rediyo don wayar da kan mutane ko da kuwa za a dage wa’adin ne.”
A bangare guda, ‘yan Najeriya na ci gaba da zaman dar-dar game da ingancin sabbin kudaden da babban bankin Najeriya ya buga.
Wasu har gwada wanke kudaden suke, domin kuwa an yada bidiyon cewa, kudaden na zubewa su koma farar takarda.