Rundunar sojin Najeriya ta ce babu sojanta ko ɗaya da aka kashe yayin fafatawar da wasu masu haƙar gwal suka yi a Ƙaramar Hukumar Jibia ta Jihar Katsina da ke arewacin ƙasar.
Cikin wata sanarwa ranar Lahadi, mai magana da yawun rundunar Janar Onyema Nwachukwu ya nemi ‘yan Najeriya su yi watsi da rahotannin da ke cewa an kashe soja biyu da kuma masu haƙar ma’adanai bakwai sakamakon rikicin da ya ɓarke a garin Magama kan gwal.
Janar Nwachukwu ya ce rahoton “ba shi da tushe” kuma “an ƙirƙire shi ne da zimmar ɓata wa sojin Najeriya suna”.
Ya ƙara da cewa babu soja ko ɗaya da lamarin ya ritsa da shi a haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba ranar 5 ga watan Janairu kamar yadda rahoton ya nuna.
Rahotanni sun ce rikicin ya ɓarke ne bayan sojojin sun ce sai an ƙara musu kuɗin da suka amince tun farko na 500,000 kan kowace mahaƙa bayan sun ga yawan gwal ɗin da aka haƙo.