Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasa da kasa IATA, ta ce kamfanonin jiragen saman nahiyar Afrika sun yi asarar dala milyan dubu 7 da milyan 700 cikin shekarar da ta 2020 gabata.
Hukumar ta ce kamfanonin sun yi wannan asara ce sakamakon tsauraran matakai da kasashen duniya suka dauka don hana yaduwar annobar corona da ta tsananta a baran.
Daraktan hukumar da ke kula da nahiyar Afrika da gabas ta tsakiya Kami Alawadi ya ce akalla ma’aikata miliyan bakwai matsalar ta shafa kai tsaye sakamakon durkushewar manyan kamfanoni 8 da ke dauke da tarin rassa da kuma miliyoyin ma’aikata a yankunan biyu.
Alawadi da ke wannan batu yayin taron manema labarai da hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta shirya kan matakan da kamfanonin za su dauka a yaki da covid-19 dama shelanta irinin barnar da annobar ta haifar musu, ya ce zai iya kai akalla shekarar 2023 zuwa 2024 gabanin dawowar al’amuran sufurin yadda s uke.
A cewar shugabar hukumar ta WHO shiyyar Afrika Dr Matshidiso Moeti, wajibi ne kamfanonin sufurin su gindaya sharuddan karbar allurar rigakafi kan duk wanda ke bukatar bulaguro a sassan Duniya.
Wannan yana daga cikin matsalolin da harkokin sufuri gami da tattalin arziki suka fuskanta sakamakon annobar cutar korona biros data addabi duniya a wannan lokaci.
Bincike ya tabbatar da cewa ba nahioyar afirka ba hatta nahiyar turai ma sun tafka babbara asara duk a dalilin wannan yanayi da ake ciki.
Zuwa yanzu dai kasar amurka ce kan gaba a yawaitar wannan cuta dama tasgwaro a fannin tattalin arziki.
Manyan kasashen turai irin su amurka, faransa da jamus wadanda ake ganin babu matsalar da zata iya kawo musu matsala a tsarin tattalin arzikin su amma yanayin da ake ciki ya jefa su cikin wani mawuyacin hali.
Zuwa yanzu dai masana tattalin arziki na ganin kusan matsalar tattalin arziki ta shafi gabadayan kasashen duniya ne.