Domin rage radadin cire tallafin man fetur, Gwamna Babagana Umara Zulum, a ranar Talata, ya gabatar da chekin naira biliyan 2 ga kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC) reshen jihar Borno don bayar da rancen da babu ruwa ga ma’aikatan da suka cancanta.
Hakan ya biyo bayan wata ganawa da gwamnan ya yi da wakilan kungiyar NLC karkashin jagorancin shugabanta na jihar, Kwamared Yusuf Inuwa.
Taron ya gudana a gidan gwamnatin Jihar da ke Maiduguri, babban birnin jihar.
Zulum ya roki NLC da ta tattauna da ma’aikatar kudi ta jihar don tantance ma’aikatan da za su samu rancen da kuma hanyoyin karbar rancen kudin ta hanyar cire akalla kashi daya bisa uku na albashi a duk wata.
Gwamnan ya kuma sanar da ware kashi 100 cikin 100 na kudaden garatuti en da ake biya a duk wata.
An kara kudin ne daga Naira miliyan 100 a duk wata, wanda ya kai Naira biliyan 1.2 a duk shekara zuwa Naira miliyan 200 a duk wata, wanda yanzu zai kai Naira biliyan 2.4.
Source: LEADERSHIPHAUSA