Shugaban kasar Gabon Ali Bongo ya ba da umarnin gudanar da binciki kan zargin da ake yi wa Patrick Assoumou Eyi, tsohon kocin tawagar kwallon kafa ta kasar ta ‘yan kasa da shekaru 17, dangane da yin lalata da matasan ‘yan wasan a lokacin da suke karkashin sa ta hanyar yi musu fyade.
Tuni dai hukumar kwallon kafa ta Gabon ta dakatar da Eyi daga bakin aiki.
Shugaba Ali Bongo, wanda ya bayyana lamarin a matsayin tashin hankali, ya baiwa ministan shari’a umarnin fadada binciken da za a gudanar kan cin zarafin kananan yara mata da maza ta hanyar fyade zuwa dukkanin nau’ikan wasanni a kasar, domin kawo karshen miyagun da suke lalata ‘ya’yan jama’a.
A wani labarin na daban an sace tubulin da Lionel Messi na Argentina ya aza a filin wasannin da Kasar Gabon ke gina wa saboda daukan bakwancin gasar cin kofin nahiyar Afrika a shekara ta 2017.
Shugaban kasar ta Gabon Ali Bongo Ondimba ya gayyaci Lionel Messi domin ya aza wannan tubulin na ginin katafaran filin wasanni dake yankin Port Gentil a ranar asabar din data gabata.
Jim kadan da sace tubulin hukumomin kasar sun kira jami’an tsaro domin su bada cikakkun bayanai kan yadda lamarin ya faru.
A bangare guda, ziyarar Messi ta haifar da cece kuce a kasar inda aka zargi gwamantin Gabon da bashi kudade har Euro miliyan 3 da rabi domin ya kawo ziyarar yayin da al-ummar kasar ke fama da kunci na rayuwa.
To sai dai fadar Shugaban Kasar ta musanta wannan zargin.
Kuma wasu na ganin irin shigar da Messi ya yi a lokacin ziyarar kamar ya nuna kaskanci ne ga mutanen Afrika inda ya sanya gajeren wando da wata karamar farar riga da zane a jikinsa.