‘Yan kasuwan mai daga kamfanin Canaf da BLCO da sauran wasu masu hada-hadar kasuwancin man fetur sun gudanar da zanga-zanga kan zargin kamfanin mai na kasa (NNPC) da babban bankin Nijeriya (CBN) wajen kawo tsaiko kan biyansu kudadens u.
Zanga-zangar ta gudana ce a ranar Laraba da ta gabata, inda suka yi dafifi a harabar shalkwatan kamfanin NNPC da ke Abuja, inda suke ta daga kwalaye masu dauke da rubutu daban-daban da ke nuna a biyasu ribarsa tare da cewa shugaban kasa yana sane da kasuwancin da suke gudanarwa.
Da yake zantawa da manema labarai, shugaban tawagar, Mohammed Abubakar ya ce, “Mu ne wakilan da ke sayar da danyan man Nijeriya ga kamfanoni masu matatun mai.”
A cewar Abubakar, suna gudanar da zanga-zangar ne domin NNPC ta baya su kudaden a kan dala biyu ga kowacce gangan mai.
“Shugaban kasa ya amince da gudanar da kasuwancinmu tun a shekarar 2018. Muna so tsohuwar NNPC ta biya mu ba sabuwa ba.”
Ya yaba wa jami’an tsaro wajen samar musu da tsaro lokacin da suke gudanar da zanga-zangan tun lokacin da suka fara har zuwa 8 ga watan Yulin 2022, lokacin da Sufeton ‘yan sanda na kasa, IGP Usman Baba ya bukaci su dakatar da zanga-zangar.
Sun bayyana akwai cikakken hujja da ke nanu cewa NNPC da CBN da gangan suka ki biyan kudaden.
“Shugaban kasa ya amince da a biya mu wadannan kudade na riba a hukumance bisa kasuwancin da kamfanonin BLCo LPFO da kuma LNG suka gudanar.
“Muna gudanar da wannan zanga-zangar ne domin sanar da duniya cewa NNPC da CBN suna amfani da sunan shugaban kasa wajen kokarin cin kudin ba tare da sanin shugaban kasa ba.”
Kamfanin ya gudanar da yarjejeniya a ranar 28 ga watan Satumbar 2021, inda ya samu amincewar karamin ministan mai, wanda ya nuna wa ‘yan jarida.
Yarjejeniyar mai take, “Mu kamfanin Canaf mun saka hannun yarjejeniya da jami’anmu, Mista Anthony Awa Mba da Mista Mohammed Abubakar domin kawo mai ga tare da BLCo da dukkan sauran abubuwan da suka shafi man fetur a Nijeriya.
“Bayan kammala dukkan hada-hadar kasuwancin, mu kamfanin Canaf mun bukaci a biya mu game da wannan kasuwanci wanda muka tura asusun banki kai-tsaye ga NNPC da fadar shugaban kasa nan take.”
Shugaban kamfanin, Mista Okwii Modekwe yana kira da kamfani NNPC da ta biya ‘yan kasuwan dala miliyan 240 daga cikin dala biliyan daya na kasuwancin da suka rattaba hannu tun a ranar 19 ga watan Yulin 2018.
Source:hausalegitng