Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewar zai taimakawa kasashen Afirka da maganin rigakafin cutar korona miliyan 15 domin yiwa jama’a rigakafi.
Turkiya ta zuba jari sosai wajen bunkasa kasuwanci da harkokin diflomasiya tsakanin ta da kasashen Afirka tun hawa karagar mulkin shugaba Erdogan a shekarar 2003.
Erdogan yace tabbas suna da labarin rashin adalcin da kasashen duniya ke nunawa Afirka wajen samun maganin rigakafin, saboda haka zai aike da maganin miliyan 15 musamman ga kasashen da ake samun karuwar masu harbuwa da cutar da kuma inda ba’a samu damar yiwa jama’a da yawa rigakafi ba.
Shugaban Turkiyan yace abin kunya ne ga Bil Adama cewar kashi 6 ne kacal na mutanen Afirka suka karbi allurar a zuwa wannan lokaci.
Erdogan yace Turkiya na aikin samar da maganin cutar korona na kan ta da ake kira Turkovac wanda ake nazari akan sa domin amincewa da shi a matakin duniya.
Rahotanni sun ce an samu karuwar masu harbuwa da cutar korona a nahiyar Afirka, inda a makon jiya kawai aka samu karin kashi 57.
Kasar Afirka ta Kudu ke sahun gaba wajen samun yawan masu harbuwa da cutar, yayin da ta zama kasa ta farko da aka gano sabon nau’in cutar da ake kira Omicron wanda aka bayyana cewar yafi saurin yaduwa daga sauran nau’oin cutar da aka gani.
Erdogan ya bayyana cewar Turkiya na shirin karfafa danganta da kasashen Afirka ta fuskar kula da lafiya da tsaro da noma da makamashi da kuma fasaha.
Shugaban dake ganawa da manema labarai bayan kammala taron, yace bangarorin biyu sun amince su yi aiki tare wajen tsara yadda zasu cimma wadannan muradu.
Cinikayya tsakanin Turkiya da Afirka ya tashi a cikin shekaru 10 daga kusan Dala biliyan 5 da rabi zuwa sama da Dala biliyan 25 bara.
Shugaba Erdogan yace a watanni 11 na wannan shekara kawai cinikayya tsakanin Afirka da Turkiya ya kai Dala biliyan 30, yayin da ya bayyana cewar Turkiya na fatar ganin an samu ci gaba zuwa Dala biliyan 75 nan gaba.
Ministan harkokin wajen Turkiya Mevlut Cavusoglu yace taron kasashen Afirka da Turkiya karo na 3 shine mafi girma, kuma ya samu halartar shugabannin kasashe 16 da ministoci 102 da kuma manyan jami’an diflomasiya 26.
Ana saran gudanar da taron na 4 a shekarar 2026.