Tsananin tashin farashin abinci, sakamakon hauhawar farashin kayayyaki, na ci gaba da yiwa ‘yan Najeriya barazana.
Lamarin da ya tilastawa iyalai su rage yawan abincin da suke ci, ko kuma su ringa tsallake cin abincin wani lokaci.
Kayan masarufi a Nigeria na tsananin tashi kamar wautar daji, inda zaka siyi abu yanzu in ka dawo ya sheda ma ya tashi.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da masana suka yi gargadin cewa har yanzu akwai barazana dan gane da illar ambaliyar ruwa ta afku a mafi yawan sassan kasar nan kan samar da abinci.
Masanan sun ce za a iya samun ‘kamarin lamarin a cikin watanni shida masu zuwa.
Binciken da jaridar Daily Trust tayi ta gano akasarin iyalai suka koma cin abinci sau biyu maimakon uku a matsayin hanyar tinkarar lamarin, wasu kuma sun tilasta kansu rage abincin da suke ci dana ‘ya’yansu.
A Ikate da ke Surulere, a wajen birnin Legas, babban birnin kasuwancin Najeriya, Doris Nwachukwu, mai sayar da kayan abinci, ta ce ta ga yadda kwastomominta ke kokawa da tsadar kayayyaki a watannin da suka gabata.
“Shinkafa, garri, albasa, indomie, komai ya tashi akan farashi. Wasu sun ninka fiye da ninki biyu, wasu sun yi tashin gwaron zabi da adai ‘kare-karen akan kowanne kaya,” inji ta.
A binciken da Daily Trust tai, ya nuna cewa garri, ‘daya daga cikin kayan abinci a Najeriya da ake siyar da shi kan Naira 500 a watan Janairun bana a kan bokitin fenti, ya kai Naira 700 a watan Maris, sannan ya haura Naira 1,100.
A halin yanzu dai bokitin fenti daya ana sayar da shi akan Naira 1,000. Haka kuma buhun shinkafar gida mai nauyin kilogiram 50 ya tashi, inda a halin yanzu ake sayar da shi kan N36,000.
A watan Janairu kuma an sayar da irin wannan adadin akan N27,000.
“Amma yawancin kudaden shiga na masu siye ba su canza ba. Mutane na korafin rashin kudi idan sun zo syen kaya.
Idan ka ce musu buhun shinkafa yanzu ya kai Naira 36,000 za su ce sun lissafa shi ne su akan Naira 30,000. sai kaga suna ta mamakin yadda ya tashi daga N30,00 zuwa N36,000 cikin kankanin lokaci.
“A wasu lokuta, abokin cinikayya na yanke shawarar ya fasa saya. Wasu da suka yi niyyar siyan kuwa sai dai su sai rabi ko kwata.
Abin da muke gani ke nan yanzu,” in ji ‘yar kasuwa Nwanchuku. Spaghetti, wanda ke zama madadin shinkafa, itama ta tashi a farashin ta.
Da Farashin kowace fakiti N150 zuwa N250, amma yanzu N350, yanzu kuma N450.