Ganawar da aka yi tsakanin Gwamnatin da da Ƙungiyar Ƙwadago ta game da batun janye tallafin mai ta tashi baran-baran ba tare da cimma wata matsaya ba.
Nasir Kabiru, Sakataren tsare-tsare na NLC ne ya tabbatar wa manema labarai hakan, inda ya ce kungiyarsu sam ba ta amince da tsare-tsaren da gwamnati ta yi ba game da janye tallafin na man fetur.
A cewarsa, bukatarsu ita ce a inganta sufuri a kuma yalwata rayuwar ma’aikata kafin a soma aiwatar da tsarin.
An dai shiga tattaunawar ce da misalin karfe 4 na yammacin yau Laraba a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Ganawar ta samu wakilai daga bangaren gwamnati da suka hada da Dele Alake, kakakin shugaba Bola Tinubu da kuma shugaban kamfanin mai na kasa (NNPC), Mele Kyari.
Sauran jami’an gwamnatin sun hada da Gwamnan Babban banki, Godwin Emefiele da tsohon gwamnan Jihar Edo, Adams Oshiomhole.
A nata bangaren, kungiyar kwadago ta samu wakilcin shugaban NLC, Joe Ajaero da shugaban TUC, Festus Osifo.
A wani labarin na daban babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ƙaryata batun cewa ya karya darajar Naira inda Dala 1 ta koma Naira 630.
CBN ya ce labarin da Jaridar Daily Trust ta bayar ba gaskiya ba ne, tunani ne kawai irin nasu.
Bankin ya ce ko a yau da safe ana sayar da Dala 1 a kan Naira 465 a kasuwar canjin kuɗi na gwamnati.
Don haka bankin ya yi kira ga ‘Yan Nijeriya su yi biris da labarin saboda ba shi da tushe balle makama.