Duk da cewa yayi zurfin karatu a bangaren kimiyya, a shekarar 1998 ya zama mamba a haddiyar kungiyar matasan sahara ta Sahrawi Youth Union gabanin hadewa da manyan kungiyoyin ta’addanci na yammacin Afrika kuma rawar ganinshi ta bashi damar shugabancin kungiyar IS a yankin.
La’akari da yadda al-Sahrawi ya yi kaurin suna wajen kai muggan hare-hare kan Soji da fararen hula kama daga na yankin da kuma Sojin ketare, hakan ya sanya shi kaurin suna ta zama cikin jerin ‘yan ta’addan da kasashen Duniya ke nema ruwa a jallo.
Jagoran na IS gabanin kisan shi a farmakin na dakarun Faransa, ya yi mulki da takalmin karfe hatta tsakanin mutanen da ke biyayya ga mulkinsa, inda ya ke yanke hannun duk wanda aka samu da laifin sata ko kuma fille kai, ko yin yankan rago ga wadanda aka samu da aikata ba dai dai ba duk dai da sunan tabbatar da dokokin addini.