Cinikayyar kasar Sin da sauran kasashe hudu na BRICS ya ci gaba da habaka cikin sauri cikin watanni 7 na farkon wannan shekara kamar yadda alkaluma suka nuna a yau Litinin.
Alkaluman hukumar kwastam ta kasar Sin sun nuna cewa, kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin daga sauran kasashen BRICS sun karu da kashi 19.1 cikin dari a tsakanin watan Janairu zuwa Yuli na bana, har zuwa kudin Sin Yuan triliyan 2.38 (kimanin dalar Amurka biliyan 330.62) idan aka kwatanta da daidai wannan lokaci na bara.
Alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, kayayyaki da kasashen suka fitar sun karu da kashi 23.9 cikin dari a shekara zuwa Yuan triliyan 1.23 idan aka kwatanta da daidai wannan lokaci na bara, yayin da kayayyakin da ake shigowa da su suka karu da kashi 14.3 cikin dari daga shekarar da ta gabata zuwa Yuan triliyan 1.15.
Cinikayya da wadannan kasashe ta kai kashi 10.1 cikin dari na jimlar cinikin waje na kasar Sin a cikin watanni bakwai na farko. Adadin ya karu da kashi 1.6 cikin dari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, a cewar hukumar kwastam.(Yahaya)
Source: LEADERSHIPHAUSA