Hukumar Gudanarwar Kamfanin Siminti na BUA, ta sanar da cewa, daga ranar 2 ga watan Oktoba farashin buhun siminti zai koma naira dubu uku da dari biyar (N3,500).
Don haka, yanzu kamfanin zai fara sayar da buhun Siminti kan naira N3,500 sabanin yadda ake sayarwa a baya kan naira dubu N5,000 a wasu wurin ma har zuwa N5,500.
A cewar kamfanin, wannan wani mataki ne na saukaka wa ‘yan Nijeriya samun damar yin gine-gine da kuma saukaka farashin kayan gini. Inda kamfanin ya ce, akwai wani sabon albishiri da zarar an kammala aikin sabbin layukan da kamfanin ke yi a halin yanzu, zuwa sabuwar shekara, kamfanin zai sake duba yiyuwar rage farashin.
A cewar sanarwar: “Dangane da bayanin da muka fitar a baya na niyyar da muke da shi na rage farashin siminti da zarar mun kammala bude sabbin layukanmu a karshen shekara, domin bunkasa kayan gini da sashin gine-gine.
“A cikin yunkurinmu na rage farashin kayayyakinmu da sake nazartar ayyukanmu lokaci zuwa lokaci, hukumar gudanarwa ta kamfanin BUA tana sanar da abokan cinikayyarta da masu ruwa da tsaki hadi da al’umma cewa daga ranar 2 ga watan Oktoban 2023, mun cimma matsayar rage farashin.
“A kan hakan, daga yanzu za a sayar da buhun simintin BUA ne a kan kudi naira 3,500 domin ‘yan Nijeriya su fara cin gajiyar farashin kafin mu kammala tsare-tsarenmu.”
A cewar sanarwar, wani karin tagomashi ma shi ne, dukkanin wadanda suka yi odar sayo simintin a kan tsohon farashi a halin yanzu, za a duba a maida shi zuwa naira 3,500 a bisa tsarin sabon farashin da zai fara aiki daga ranar 2 ga Oktoba.
Kamfanin ya shawarci dillalanta da su tabbatar jama’a sun amfana da wannan sabon farashin kuma kamfanin zai sanya Ido wajen ganin an bi umarnin amfani da sabon farashin ba tare da tangarda ba.
Idan za a iya tunawa dai Shugaban rukunin kamfanin BUA, Abdul-Samad Rabiu, a kwanain baya lokacin da ya ziyarci shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, ya sanar da cewa, kamfanin ya shirya tsaf domin rage farashin Siminti a Nijeriya zuwa naira N3,500 ko ma kasa da haka.
Source LEADERSHIPHAUSA