Wani dan kasuwa mai suna Shuaibu Mahammad, wanda ke da karamin shago a Kasuwar singa, ya ce ya yi mamakin hauhawar farashin kayayyaki a kullum.
Ya ce yanzu ya daina sayan kayan abinci da yawa saboda yadda jarinsa ya zama da kuma tsoron karma tashin kayyyaki yasa ya daina kasuwanci.
“Yanzu ina sayarwa ne mudu-mudu sabida ‘yan uwana talakawa su zo su ringa auna”.
“Farashin yana ci gaba da ‘karuwa kowace rana. Hakika wannan yana shafar mu.
Yawancin ƴan kasuwa da yawa sun na shan wahala wajen ciyar da iyalansu.
Wata bazawara kuma mahaifiyar ‘ya’ya hudu Habiba Sama’ila ‘yar shekara 40, ta ce tashin farashin kayan masarufi, tare da mutuwar mijinta a ‘yan shekarun da suka gabata, ya tilasta mata barin duk wata sana’a, saboda duk jarinta ya kare wajen ciyarwa. iyali.
“Al’amura suna faruwa a kowace rana
Ba mu kuma tunanin wani abu sai abinci, kuma ‘kudin sa sai ‘karuwa yake, Mutane irina da ba su da mai tallafa musu suna cikin matsala,” in ji ta.
Abin da ke faruwa a Ikate (Lagos) da Singa (Kano) lamari ne da ya zama ruwan dare gama gari a Najeriya yayin da farashin kusan duk wasu kayayyakin gida da aka sani ya tashi.
Wannan hauhawar farashin ya cutar da talakawa, in ji Dokta Muda Yusuf, shugaban cibiyar kasuwanci mai zaman kanta kuma tsohon darakta-janar na kungiyar ‘yan kasuwa da masana’antu ta Legas.
“Kamar yadda kuke gani, abubuwan da iyalai ke amfani dashi a gidajensu yanzu ya karu da da kashi 70 cikin 100, wasu ma ya kai kashi 80 cikin 100 saboda dole ne ka ciyar da iyalinka,” Yusuf ya yi nuni da cewa, ‘daya daga cikin abubuwan da ke haifar da hakan shi ne ‘karuwar fatara a Najeriya, inda mutane da dama shiga ‘kangintalauci.
“Idan har za a yi maganin wannan matsalar ta talauci, sai an magance matsalar hauhawar farashin kayayyaki, ta yadda talaka zai samu akalla ya sayi wani abu a cikin sauki da zau iya sarrafawa”.
Dalilan hauhawar farashi Hauhawar farashin kayayyaki ya samo asali ne daga abubuwa da dama, na gida da waje, in ji Dokta Yusuf.
Ya bayyana rashin tsaro a matsayin babban dalilin tashin farashin kayayyakin abinci, sai kuma tabarbarewar ababen more rayuwa da suka hada da sufuri da wutar lantarki.
“Dalilin da ya sa abubuwa suka yi muni sosai a Najeriya shi ne rashin tsaro. “
Kusan kashi 90 cikin 100 na harkar noma, ana yi ta hanyar gargajiya, amma kuma ga yadda al’umma na karuwa”. inji Dakta yusuf.
Hukumar ta NBS ta dora alhakin hauhawar farashin kayayyaki da ake shigowa da su daga kasashen waje, sakamakon faduwar darajar kudin kasar nan.
Sai dai Yusuf ya ce: “Farashin kayan abinci zai kara tashin gwauron zabi sabida tasirin ambaliyar ruwa da aka tafa”.