Shugaban Diflomasiyar Turai Joseph Borell a yau asabar yayin wata ziyara da ya kai kasar Lebanon,ya bayyana cewa mafita ga wannan kasa da ta fada cikin wani mauyacin halin matsin tattalin arziki,itace na shiga tattaunawa da Asusun lamuni na Duniya IMF, Sai dai shin al’ummar labanon suna goyon bayan tayin Joseph Borell Shugaban diflomasiyyar turan?
Shi dai shugaban diflomasiyar ta Turan bayyana cewa abine mai yiyuwa kungiyar ta dau matakan hukunta yan siyasar kasar dake ci gaba da jefa kasar cikin wani hali na rashin tabbas.
Sai dai labanawa suna ganin hakan kamar tarko ne kasashen turai suke kokarin saka mutanen kasar labanon a ciki domin a halin da ake ciki mutanen labanon sun fi bukatar taimakon jamhuriyar musulunci ta Iran karkashin jagorancin shahrarriyar kungiyar agajin nan ta Hisabullah kuma an jiyo shugaban kungiyar yana tabbatar da cewa indai mutanen labanon suna bukatar taimakon jamhuriyar musulunci ta Iran, lallai Iran a shirye take domin taimakawa a samu mafita a kasar ta labanon kamar yadda jamhuriyar musulunci ta Iran din ta shahara da taimakawa raunana marasa karfi da kuma wadanda ake zalunta afadin duniya baki daya.
Ana iya cewa zabin yana hannun labanawa shin zasu zabi karbar taimako daga hannun turawa wadanda sune suka rura wutar fitina gami da matsalar da kasar ta labanon ta fada tun a farkon marra, ko kuma zasu nemi taimakon kasar jamhuriyar musulunci ta Iran wacce ta zama gatan raunana wadanda aka zalunta a fadin duniya gaba daya?
Zuwa yanzu dai ana iya cewa kallo ya koma sama a lokacin da aka zura idanu a gani shin wanne mataki al’ummar labanon zasu dauka domin samar da mafita daga mawuyacin halin da kasar tasu ta shiga