Shugaban kasar Tunisia Qais Saeed ya bayyana cewa, ya dauki wannan matakin ne saboda maslahar kasar, da kuma kokarin ganin an ceto ta daga durkushewa, bayan kasawar gwamnatin Firaministan Hesham Mechichi, wajen gudanar da ayyukan da suka rataya a kanta wanda al’ummar kasar ke jiran gani daga gare ta.
Daya daga cikin dalilan shi ne kasa shawo kan matsalar sabuwar cutar corona, ko kuma daukar matakan da suka dace domin dakile matsalar, wadda take lakume rayukan jama’a a kasar.
Baya ga haka kuma shugaban na Tunisia ya bayyana majalisar dokokin kasar da cewa, tana aiwatar da manufofin jam’iyyu e kawai, musamman ma wadanda suka yi babakere a cikin majalisar, maimakon yin aiki da jama’a suke bukata.
Sai dai mataki na shugaban Tunisia ya fuskanci kakkausan martani daga wasu jam’iyyun kasar, musamman jam’iyyar Nahda, yayin da kuma a daya bangaren jama’ar gari da dama suka bayyana gamsuwarsu da wannan mataki.
A wani labarin na daban a rahoton kamfanin dillancin labaran iqna, zababben shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran za ta ci gaba da goyon bayan alummar Falasdinu, a gwagwarmyan da suke yi da yahhttps://iqna.ir/ha/news/3486147/wasu-sabbin-sharuddan-saudiyya-kan-ayyukan-umrahudawan Sahyoniyya wadanda suka mamaye kasarsu.
Ra’isi ya bayyana hakan ne a zantawa ta wayar tarho da ya yi da shugaban kungiyar Hamas a bangaren siyasa Isam’ila Haniyya da kuma babban sakaren kungiyar Jihadul Islami Ziyad Nakhala a jiya Talata.
Sayyid Ibrahim Ra’isi ya kara ta ya al-ummar Falasdinu nasarar da suka samu a fafatawa ta karshe da yahudawan Sahyoniyya na kwanaki sha daya.
Sannan a nashi bangaren Isama’ila Haniyya ya taya Sayyid Ra’isi murnar zabensa a matsayin shugaban kasar Iran, ya kuma yi masa fatan alkhairi a ayyukasa.
Hakama Ziyad Nakhala ya taya zabebben shugaban murnar zabensa da kuma fatan All..ya bashi damar sauke nauyin da aka dora masa, sannan ya kara godiya ga Iran kan tallafin da take bawa al-ummar Falasdinu a gwagwamayar da suke yi da yahudawan sahyuniya.