Cikakkiyar sa’a guda bayan alkalin wasa Anthony Taylor ya busa usur din tashi wasa, magoya baya sun yi ta hayaniya da ba ya misaltuwa
Daruruwan magoya bayan sun zabi kada su bar filin wasan har sai kungiyar ta karbi bukatarsu ta neman Ronaldo ya gana da tashar talabijin.
Bayan Cristiano Ronaldo ya amsa wannan kira ne aka ci gaba da sowa ta murna da jinjina gad an wasan.
Ronaldo ya ci kwallaye 118 a wasanni 292 da ya buga wa Manchester united daga shekarar 2003 zuwa 2009, lokacin da ya koma Real madrid a kan kudi Fam miliyan 80.
A cikin shekaru 12, ya ci kwallaye 551 a real Madrid da Juventus, kafin ya yin a Unikted kome mai ban mamaki a kan kudi fam miliyan 12.8.
Cristiano Ronaldo ya yi cikakken atisaye a wannan Laraba gabanin wasan farko da zai sake buguwa Manchester United tun bayan da ya sake yiwa kungiyar kome.
A wannnan Laraba yayi cikekken atisaye don United ta samu damar tantance ko a shirye yake ya taka rawa a ziyarar da Newcastle za ta kai Old Trafford ranar Asabar a gasar Premier.
Wannan shine karon farko da Ronaldo ya sake leka filin atisayen United tun bayan barin kulob din shekaru 12 da suka gabata zuwa Real Madrid kan farashi mafi tsada a wancan lokacin wato fan miliyan 80.