Gwamnatin jihar Kano ta maka gwamnatin tarayya a gaban wata babbar kotun jihar bisa abin da ta bayyana a matsayin cin zarafi da hukumomin gwamnatin tarayya uku masu yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa suka yi wa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar (PCACC).
Wannan ya biyo bayan gayyatar da Hukumar EFCC, ICPC da takwararsu ta kula da da’ar ma’aikata CCB suka aike wa Hukumar PCACC da shugabanta, Muhuyi Rimingado domin amsa tambayoyi kan yadda Hukumar ta gudanar da ayyukanta tun daga shekarar 2011 har zuwa yau.
A wani umurni na musamman, kotun karkashin jagorancin mai shari’a Farouk Adamu, ta umurci gwamnatin tarayya da hukumominta da su dakatar da duk wani yunkurin binciken hukumar PCACC da shugabanta.
Kotun ta kuma umarci hukumomin da su daina tsoma baki cikin harkokin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar (PCACC).
Umurnin mai lamba K/M1128/2023, ya kuma shawarci dukkan bangarorin da abin ya shafa da su kiyaye matsayinsu.
A wani labarin na daban kwamitin da gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri, ya dora wa alhakin raba kayayyakin abinci da rage radadi, biyo bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi, ya bayyana tsare-tsaren ganin rabon ya kai ga mutanen da suka fi bukata.
Da yake jawabi jim kadan da kammala ganawar da mambobin kwamitin suka yi a Yola a ranar Litinin, sakataren gwamnatin jihar Awwal Bamanga Tukur, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin, ya ce za su tabbatar da gaskiya da adalci a rabon.
Ya ci gaba da cewa “shirin zai shafi harkokin jama’a ta kowane bangare, musamman tafiye-tafiye, rage kudaden farashin kayayyakin abinci da kashi 50 bisa dari, a daukacin cibiyoyin kada kuri’a 266, a fadin jihar.
“Shirin zai kawo saukin tafiye-tafiye ga ma’aikata, ‘yan makaranta, masu kananan karfi da matafiya da ke shigowar jiha, kan haka mun samar da motocin bas-bas 10 daga kamfanin Innoson a kan kudi naira biliyan 1.06”.
Tukur, ya ce manufar shirin shi ne kawo sauki ga wahalhalun da jama’a ke ciki, ya ce “mutane mabukata kamar; matan da mazajensu suka mutu, matan da aurensu ya mutu, nakasassun mutane, makarantun kwana da kungiyoyin mata da matasa su za su amfana da shirin, za mu tabbatar kowa ya amfani” in ji Bamanga.
Haka kuma sakataren gwamnatin jihar Awwal Tukur, ya ce gwamnatin jihar ta karbi tallafin naira miliyan dubu biyu, daga gwamnatin tarayya, kari kan tirelan biyar na shinkafa, yabce ita ma gwamnatin jihar ta samar da tirela 50, na shinkafa da masara.
“Bisa umarni, za mu tabbatar da jama’a sun samu sauki, za mu tabbatar farashinmu ya karya farashin abinci a kasuwa, za mu sayarda karamin buhu a kan kudi naira dubu 10, ba kamar yadda yake a kasuwa dubu 20 ba” in ji Bamanga.
Shugaban kwamitin ya ce kwamitin yana da masu sa ido game yadda shirin zai ci gaba da gudana, ya roke ‘yan jaridu da su rika bibiyan aikin kwamitn, ana dai tsamammin za a fara aikin a ranar Laraba.