Wani ‘dan Najeriya mai suna Wale Oladapo ya koma da zama Canada a 2016 kuma ya bude gidan biredi bugun kato a kasar.
Biredin ya kasance mai taushi wanda jama’a da dama suke yabawa kuma ya yadu har zuwa yankunan kasar.
Yace akwai rassan gidan biredin a Waterloo, Windsor, Ottawa da Calgary yayin da wasu suka karba sunan suna yin irin shi.
Kwastomomi a Canada sun yabawa wani gidan biredi na ‘dan Najeriya mai suna Grey Matlock Bakery da ke Brampton, Ontario kan yadda yake yin biredi bugun kato mai laushi.
Shi dai irin wannan biredin a arewacin Najeriya ana kiransa da Bugun kato yayin da kudanci ake kiransa da biredin Agege, wani yankin jihar Legas.
Biredi mai matukar taushi.
‘Dan Najeriya mai suna Wale Oladapo ya bude gidan biredin a Brampton bayan komawa Canada da yayi a 2016.
Sai dai ya bude shi a shekarar 2018 kuma ya matukar fadada shi zuwa yankuna daban-daban na kasar Canada.
Kamar yadda yace, gidan biredin ya yadu har zuwa yankunan Calgary, Waterloo, Ottawa da Windsor inda kuma wasu suka karba sunansa suna yin irin biredin.
Sarkin Brampton ya ziyarci gidan biredin wanda tun daga nan labarinsa ya yadu kuma ake ta bayyana irin karbuwar da yayi.
Matar aure ta haifa yaro da IUD rike a hannunsa
A wani labari na daban, wata matar aure mai suna Violet ta sanar da yadda ta samu ciki duk da tayi tsarin iyali.
Tace sun yi aure da mijinta amma basu shirya haihuwa ba, hakan yasa ta je ta saka IUD a cikin mahaifarta saboda kada ta dauka ciki.
Violet tace ta fara amai da zazzabin dare kuma hakan yasa ta zabura ta yi gwajin ciki.
Cike da abun mamaki wannan gwajin ya nuna tana dauke da juna, dole ta sa ta bar cikin duk da bata shirya haihuwa ba.
Violet ta sanar da cewa, cikinta ya tsufa kuma nakuda ta tashi wanda ta garzaya asibiti.
Amma cike da abun mamaki ta haifa yaro namiji sai dai yana rike da IUD din a hannun.
An tattaro malaman jinya na asibitin wanda suka zo suka dinga ganin abun mamaki.
Source:LegitHausa