Wata kotu mai zama a Abuja ta yanke hukunci bayan kame Doyin Okupe da cinye kudin gwamnati ba bisa ka’ida ba.
An daure Okupe tsawon shekaru biyu a gidan yari bayan kama shi da laifuka sama da 50 da aka kawo gaban kotu.
Hukumar EFCC ce ta gurfanar dashi bisa zargin ya saci N702m da ya karba a hannun mai ba tsohon shugaban kasa shawara.
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta daure darakta janar na gangamin kamfen Peter Obi bisa kama shi da laifin karkatar da kudin kasa, TheCable ta ruwaito.
Hukumar yaki cin hanci da rashawa ta EFCC ce ta gurfanar
Doyin Okupe tun shekarar 2019 bisa zarginsa da wasu laifuka 59 da suka hada da karkatar da kudaden kasa da yawansu ya kai akalla N702m.
An gurfanar dashi a gaban mai Ijeoma Ojukwu ne tare da wasu kamfanoni biyu; Value Trust Investment Ltd da Abrahams Telecoms Ltd – da ake zargin suna da hannu a badakalar.
An yi zargin cewa, Okupe ya karbi kudin ne daga ofishin Babban mai ba shugaban kasa shawari kan harkokin tsari (NSA) a lokacin da Sambo Dasuki ke kan kujerar.
Da take yanke hukunci a ranar Litinin 19 ga watan Disamba, Ojukwu ta ce ta kama Okupe da laifi bisa tanadin sashe na 16(1) da (2) na kudin dokar halatta kudin haram bisa karbar kudi tsaba a hannu na hara..
A cewar mai shari’a, NSA ba cibiyar kudi bane shi, kuma duk da cewa tsohon shugaban kasa Jonathan ya sanya hannu kan ba da kudin, bai bayyana adadin da yace a bayar ba, wanda hakan ya saba dokar halatta kudin haram.
A cewarta: “Na kama wanda ake kara, Dr. Doyin Okupe, a kan laifi na 34, 35, 36 zuwa 59.”
Bayan cikakken bayani, mai shari’a Ojukwu ya daure Okupe shekaru biyu a gidan yari, kamar yadda rahoto ya bayyana.
Tsohon Shugaban Kasa Ya Fadi Babban Abin da Yake Sa Jami’ai Tafka Sata a Gwamnati.
A bangare guda, tsohon shugaban kasa Jonathan ya bayyana dalilin da yasa ma’aikata da jami’an gwamnati ke satan kudi daga lalitar kasa.
A cewarsa, da yawan ma’aikatan gwamnati na duba da yadda rayuwarsu za ta kasance ne bayan sun yi ritaya, kasancewar kudaden fansho basu da tsoka ga kuma ba sa samuwa da wuri.
Ba sabon abu bane a Najeriya tsoffin ma’aikata su fito domin yin zanga-zanga kan rike musu ‘yan kudaden fansho da suke bin gwamnati.