Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, ya ce yawancin ‘yan siyasar da ke neman kujerar shugabancin kasar a zaben shekara ta 2023, kamata yayi su kasance garkame a gidan yari.
Yanzu haka dai, wadanda ke kan gaba a tsakanin wadanda suka bayyana aniyar neman hawa kujerar Shugabancin Najeriya a zabe mai zuwa, sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da tsohon gwamnan Legas, Ahmed Bola Tinubu, da kuma tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki.
Bikin na zagayowar ranar haihuwar tsohon shugaba Obasanjo ya samu halartar manyan baki cikinsu har da shugabar Hukumar Kasuwanci ta Duniya WTO Dakta Ngozi Okonjo-Iweala, da kuma shugaban bankin raya kasashen Afirka AFDB Dakta Akinwumi Adesina.
A wani labarin na daban Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi barazanar katse ci gaba da kasancewar Ukraine a matsayin yantatar kasa, a yayin da mamayar da ya yi wa kasar ke ci gaba da gamuwa da turjiya, kuma tattalin arzikin kasarsa ke dada dankwafewa sakamakon takunkumai masu gauni.
Rasha ta ci gaba da kai hare hare Ukraine, amma shugaba Zelensky wanda ke turjewa ya ce dakarunsa na mayar da zazzafan martani a yankin Kharkiv, birni na biyu mafi girma a kasar, kuma su ma maharan na dandana asarar da ko a mafarki ba su taba gani ba.
Shi ma ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba cewa yake, jini na kwarara daga Ukraine, amma sam, ba ta fadi ba, yana mai cewa asirin sojin Rasha da ke da karfin gaske ya tonu.