A halin yanzu gwamnatin tarayya ta amince Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya NPA ta samar da sashi na musamman da zai rinka kulawa da kayyakkin da aka shirya fita da su kasashe wajeta jiragen ruwa wanda aka yi lakabi da (Edport Processing Terminal (EPT), kamfanin AIM Logistics Limited ne aka ba kwangilar gudanar da wannan sashi, wanda hakan zai kawo sauki sosai wajen shiga da fitar kayayyaki daga cikin kasa.
Sashin zai kasance ne as kan babbar hanyar Legas zuwa Shagamu, kuma tuni aka ba kamfanin takardar izinin fara aiki bayan da jami’an hukumar NPA suka kai ziyarar ganin yadda wurin yake da irin kayan aikin da suke da shi.
Shugaban Hukumar Tashoshin Jiragen Nijeriya NPA, Mohammed Bello Koko, ya bayyana cewa, wannan amincewar zai kara taimakwa wajen cimma kudurin gwamnatiun tarayya na karfafa tattalin arzikin kasa, za a kuma hada hannun da hukumar karfafa shiga da fitar kayayyaki kasashen waje (Nigerian Edport Promotion Council (NEPC) da sauran hukumomin da suke da dangantaka da harkar shiga da fitar da kayayyaki a Nijeriya.
Shugaban NPA ya kuma kara da cewa, wannan sashin zai zama wajen da za a rinka shirya kayayyakin da za a fitar da su, musamman kayan gona a nan kuma za a rinka bayar da izini da amincewa da ingancin kaya kafin a wuce da su tashar jirgin ruwa.
Shugaban kamfanin AIM Logistics Limited, Jide Adeleye, ya ce kamfaninsu na da kayan aiki na zamani kuma za su tabbatar da gudanar da aiki yadda kamata daidai da abin da ake yi a kasashen duniya, ya kuma mika godiyarsa ga shugaban NPA, Bello Koko a kan yadda yake gudanar da harkokin hukumar, ya yi addu’ar Allah ya taimake shi a dukkan harkokinsa.
Source LEADERSHIPHAUSA