Kamfanin man fetur na Nijeriya, NNPCL, ya gargadi jama’ar kasar da su kiyayi sayen mai suna adanawa, don tsoron fuskantar karanci da karin farashin man.
BBC ta rawaito cewa, gargadin ya biyo bayan karuwar jerin motoci ne a gidajen mai a sassan kasar a ‘yan kwanakin nan.
NNPC Limited, ya ce yin gargadin ya zama wajibi, bisa la’akari da yadda aka fara ganin layukan ababen hawa a gidajen mai a birnin Ikko, cibiyar kasuwancin kasar, da birnin tarayya Abuja da dai sauran wasu garuruwa na Nijeriyar.
Wata sanarwa da kamfanin man ya fitar, ta ba wa ‘yan Nijeriya tabbaci, cewa an gano bakin zaren dangane da abin da ya haddasa layukan ababen hawa a gidajen man.
NNPCL, ya ce abin da ya janyo wannan matsala shi ne raguwar dakon man daga ma’ajiyarsa da ke Apapa a birnin Ikko, wato Legas.
Amma yanzu haka akwai isasshen mai a adane, wanda aka yi amanna za a kwashe tsawon kwana talatin ana amfani da shi a kasar, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Saboda haka, kamfanin man na Nijeriya ya yi gargadin cewa, jama’a su guji sayen man suna adanawa, bisa tsoron za a yi fama da karancinsa.
NNPCL, ya ce, nan da ‘yan kwanaki kadan komai zai daidaita game da safararsa zuwa sassan Nijeriyar.
Ana fatan wannan sanarwa da kamfanin man ya bayar, za ta kwantar wa jama’ar kasar hankali, ta kuma kawar da duk wata fargabar da ake yi, cewa mai yiwuwa an hau hanyar fama da karancin man, ko kuma an fara take-taken da za a kara farashinsa.
Source LEADERSHIPHAUSA