Wahalar Rayuwa: Masa sun wawashe kayan abinci a tirela
Abin ya faru a jiya a jihar Neja, inda wasu fusatattun matasa suka shiga wawason wasu kayan abinci dake cikin tireloli, abinda yasa jami’an tsaro sukayi kokarin tarwatsa su da karfi.
A ranar juma’a jaridar Leadership ta tattaro cewa matasan sun tare tirelolin da suke hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Kamar yadda aka tattaro matasan sun kona tayoyi a kan hanya inda suka fara dibar kayan abincin wanda suka hada da hatsi shinkafa da kuma wake kafin jami’an tsaro su shiga tsakani ta hanyar harbi a sama domin tarwatsa matasan.
A ta bakin wani matashi dake hanyar Kaduna wanda ya bukaci a sakaya sunan sa ya bayyana cewa, tuni matasan sunyi awon gaba da buhunan hatsi kafin shiga tsakanin da jami’an tsaro sukayi.
Wata majiya ta jaridar Leadership ta bayyana da mai tushe ta tabbatar da cewa masu baburan hawa ne suka shirya zanga zangar domin nuna adawa da wasu masu karbar kudede da masu tattara kudin shiga sukeyi inda matasan sukayi amfani da wannan dama domin wawashe kayan abincin da tirelolin suka dauko.
Duba : Abinda Sanata Shehu Sani Yace Kan Wani Malami
Ko hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar Neja ma Wasi’u Obiodun ya tabbatar da cewa, anyi zanga zanga a hanyar Kaduna zuwa Abuja yau amma ba’a sanar da ‘yan sanda ba