Dakarun kungiyar tsaro ta NATO sun fara gudanar da wani gagarumin atisayen soji a kasar Norway.
Jiragen yaki na sama kimanin 200 da kuma jiragen yakin ruwa 50 na cikin atasayen sojojin na kasashen NATO, wanda zai kai har zuwa ranarNATO 1 ga Afrilu kafin a kammala shi.
Matakin ya zo ne a daidai lokacin da duniya ta shiga zaman dar dar sakamakon yakin da Rasha ta kaddamar kan Ukraine, inda take cigaba da kai hare-hare a sassan kasar, domin hana makwafciyar tata kasancewa mamba a NATO, da a yanzu ta kaddamar da atisayen soji.
A karshen makon da ya gabata dai Rasha ta tsananta hare-haren da take kaiwa cikin Ukraine, wannan karo a bangaren arewaci da kuma yammacin kasar, yayin da alkalumma ke cewa mutane 35 sun rasa rayukansu a daya daga cikin hare-haren jiragen yakinta suka kai barikin Lviv kusa da iyakar Ukraine da Poland.
To sai dai a sanarwar da ta fitar, ma’aikatar tsaron Rasha ta ce ta kashe sojin haya ‘yan asalin kasashen ketare akalla 180 ne ne a lokacin da suke kokarin shiga Ukraine daga iyakar Poland.
A wani labarinna daban Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi gargadin cewa duk kasar da ta nemi sanya dokar hana shawagin jirage a sararin samaniyar Ukraine, gwamnatinsa za ta dauke ta a matsayin wadda ta shiga yaki da ita kai tsaye.
Wannan gargadi dai ya zo ne sa’o’I kalilan bayan da, kungiyar tsaro ta NATO ta yi watsi da bukatar Ukraine na hana zirga-zirgar jiragen sama a sararin samaniyarta, abinda ya janyo kakkausar suka daga shugaban kasar Volodymyr Zelenskyy, wanda ya ce matakin ya baiwa Rasha karin damar cigaba da yi wa kasarsa ruwan bama-bamai.
Sakatare Janar na NATO Jens Stoltenberg ne ya sanar da matakin kin amincewa da haramta zirga-zirgar jiragen sama a Ukraine, bayan wani taron gaggawa na kasashe 30 da ya jagoranta a Brussels.
Kawo yanzu kididdiga ta nuna cewar, fiye da ‘yan Ukraine miliyan 1 suka tsere daga kasar, kuma dubu 780,000 daga cikinsu sun tsallaka ne cikin Poland, tun bayan da Rasha ta fara mamaye kasarsu a ranar 24 ga watan Fabrairu.