Hukumar Kula da yanayi a Najeriya ta ce nan da kwanaki 3 masu zuwa mazauna wasu Jihohin kasar da suka hada da Kano da Jigawa da Kaduna da Bauchi da Plateau da Yobe da Gombe da kuma Borno za su fuskanci ruwan sama mai yawa, abin da ya zama gargadi ga mazauna wadannan jihohi.
Sai dai Hukumar Najeriya ta ce sabanin wadancan kasashe, mazauna Jihohin da ake saran su samu ruwan madaidaici sun hada da Katsina da Abuja da Kebbbi da Neja da Kwara da Kogi da Nasarawa da kuma Adamawa.
Sauran sun hada da Taraba da Benue da Cross River da Oyo da Ogun da Lagos da Osun da Ondo da Edo da Ekiti.
Sai kuma Delta da Bayelsa da Akwa Ibom da Imo da Ebonyi da Enugu da Anambra.
A wani labarin na daban Mali ta zargi sojojin Faransa da yi mata leken asiri a lokacin da suka yi amfani da wani jirgi mara matuki wajen daukar hoton abin da Faransa ke zargin sojojin haya ne ke binne gawarwaki a kusa da wani sansanin soji.
Kwana daya da faruwar hakan, sojojin Faransa sun watsa wani faifan bidiyo da ta ce ya nuna sojojin hayar Rasha suna rufe gawarwaki don zargin sojojin Faransa da suka fice da aikata laifin.
Da sanyin safiyar Talatar nan ne dai rundunar sojojin Mali ta sanar da gudanar da bincike kan gano wani kabari da aka yi a sansanin na Gossi.
Rundunar ta ce ta gano kabarin ne washegarin da aka wallafa hotunan.
Mali dai ta zargi Faransa da yin leken asiri da kuma yunkurin bata sunan sojojin ta da bidiyon da aka dauka da jirgi mara matuki.
Kakakin gwamnatin kasar Abdoulaye Maiga ya ce, anyi amfani da jirgin maras matuki ne domin yin leken asiri ga dakarun sojin Mali.