Da alamun gwamnatin tarayya ta yi kasa a gwiwa wajen wayar da kan jama’a kan lamarin sabon Naira.
Saura kiris a yiwa wani mutum tumbur a gidan abinci yayin da yayi kokarin biyan kudin abinda ya saya da sabon Naira.
Kakakin bankin CBN ya ce bankin na iyakan kokarinta wajen wayar da kan al’ummar karkara.
Saura kiris a yiwa wani dan Najeriya tumbur a gidan abinci yayinda yayi kokarin biyan kudin abincin da yaci da sabuwar takardar N1000 da babban bankin Najeriya CBN ya buga.
Mutumin ya shiga gidan abincin kuma ya cika cikinsa, yayinda yake kokarin biyan matar mai gidan abinci da sabon N1000, ta ce sam bata san da wannan kudin ba.
A bidiyon da ya bazu a shafin Tuwita ranar Juma’a, matar ta cakumesa kuma ta hana shi tafiya har sai da ta yaga masa wando ta kusa yi masa tsirara a bainar jama’a.
A faifan bidiyon, wata mata ta yi kokarin fadakar da mai gidan abincin cewa sabon kudi ne amma matar ta ki.
Ta cigaba da cewa lallai sai ya biyata da tsohon kudin da ta sani.
Ta ce: ” Ka biyani kudi na, wani irin rainin hankali ne wannan.”
“Ni ban taba ganin irin wannan kudin ba, kuma ba zan karba ba.”
Shi kuma mutumin yace: “Wannan sabon Naira ne.”
Cikin kankanin lokaci matar ta tara masa jama’a kuma ta fara yunkurin kiransa da barawo.
Wannan na nuni karara cewa babban bankin CBN bai wayar da kan jama’a yadda ya kamata ne gashi saura wata guda da a daina amfani da tsohon Naira.
Kalli faifain bidiyon: Martanin CBN Yayinda aka tuntubi Kakakin bankin CBN, Osita Nwanisobi, ya bayyana cewa bankin na iyakan kokarinta wajen wayar da kan yan Najeriya kan sabbin takardun Naira, rahoton PremiumTimes.
Ya ce zasu hada kai da hukumar NOA domin zurfafa wayar da kan jama’a musamman wadanda ke karkara basu da labarin halin da ake ciki a birni.
Yace: “Muna kokarin cigaba da wayar da kan mutane, kuma muna hada kai da hukumar wayar da kai saboda kowa ya samu labari, har da karkara.”