Gwamnatin jihar Kaduna ta bada tabbacin hada hannu da malaman addini domin magance kalubalen talauci da ake fuskanta na sama da kashi 80 cikin 100 a yankunan karkara, za kuma ta mayar da yaran da basu zuwa makaranta ajujuwa domin samun zaman lafiya da cigaba a fadin jihar.
Gwamnan jihar, Malam Uba Sani ne ya bayyana hakan a yayin wani taro da kwamitin addini na jihar Kaduna, domin inganta zaman lafiya da inganta tsaro da aka gudanar a Kaduna.
Gwamna Sani ya roki malaman addinin Musulunci da na Kirista da su tallafawa gwamnati ta hanyar wa’azin wanzar da zaman lafiya a tsakanin mabiyansu.
Ya ce, ba za a iya samun zaman lafiya da tsaro a jihar ba, matukar kashi 80 cikin 100 na ‘yan jihar, musamman a yankunan karkara na fama da matsanancin talauci.
A cewarsa, akwai yara sama da 600,000 da ba sa zuwa makaranta a jihar, don haka, ya zama dole ne a mayar da su makaranta domin samun zaman lafiya a jihar.
“Muna fuskantar matsaloli na fama da matsanancin talauci musamman a yankunan karkara. Kashi 80 cikin 100 na mutanen karkara na fama da matsanancin talauci. Wannan shi ne Gaskiyar magana.
“A watan da ya gabata, mun fara aikin gina tituna 32 a fadin jihar, wadanda akasarinsu na yankunan karkara ne.”
Gwamna Uba Sani ya kuma bayyana cewa, daga mako mai zuwa, gwamnatin jihar Kaduna za ta fara gina makarantu 100 domin mayar da yaran da ba sa zuwa makaranta ajujuwa domin magance matsalar rashin zuwa makaranta.
“An bar yara ba sa zuwa makaranta, suna yawo a kan tituna kuma a ce ana son a magance matsalar rashin tsaro? Ba zai yi wu ba. Don haka, dole ne a mayar da su makaranta.
“Bincikenmu ya nuna cewa, saboda talauci ne yawancin yaran ba su zuwa makaranta. Mutanen karkara ba sa tura ‘ya’yansu makaranta domin suna son su je gona ko kuma su tafi talla. Don haka, idan ba mu rage talauci daga kashi 80 cikin 100 zuwa akalla kashi 30 cikin 100 nan da shekaru masu zuwa ba, ba za mu taba iya magance matsalar yaran da ba su zuwa makaranta.”
Gwamnan ya jaddada cewa, dole ne gwamnatin ta farfado da tattalin arzikin yankunan karkara ta hanyar samar da ayyukan yi domin kawo karshen talauci.
Malam Uba Sani ya kuma bayyana cewa, gwamnatin Kaduna za ta hada kai da malaman addini wajen samar da bayanan marayu 5,000 a jihar domin basu tallafin karatu da gidauniyar tallafi ta Qatar ke daukar nauyi.
Source LEADERSHIPHAUSA